Min menu

Pages

An samu gareji wanda mata ne zalla ke gyara ababan hawa

 Wani gareji na farko da aka taba yi a Nijeriya wanda mata ne zalla ke aikin gyara ababan hawa.Wata kungiyar gidauniyar tallafawa mata ce dai ta bude wannan garejin a jihar sokoto.


Gareji dai a Nijeriya kowa yasan maza ne kanikawa to amma yanzu an samu wani gareji da mata ne zalla a ciki kuma sune ke aikin gyara motoci da sauran ababan hawa.


Hakika wannan abin mamaki ne da yaja hankali sosai musamman da garejin a Nijeriya yake kuma arewa.


Mutane da dama sun jinjinawa wanda ya bude garejin kuma sun sake jinjinawa matan dake aikin a garejin.Wasu da dama sun goyi baya yayinda da dama daga cikin mutanen suka nuna rashin dacewar abin.


Gidauniyar data tallafawa wadannan matan sunanta NANA.

Saidai abin birgewa game da wadannan matan shine koda yaushe suna sanye da hijab


Comments