Min menu

Pages

RUNDINAR SOJIN NIGERIA TA GARGADI DR AHMAD GUMI

RUNDINAR SOJIN NIGERIA TA GARGADI  DR AHMAD GUMI


Rundinar sojin Nigeria ta fiyar da sakon gargagi ga jarumin Malaminmu Sheikh Dr Ahmad Gumi akan abinda ya fada cewa wasu daga cikin sojojin da ba Musulmi ba suna kisan gilla wa 'yan uwa Musulmi fulani makiyaya


Rundinar sojin tace Dr Ahmad Gumi ya kiyayi kokarin raba kan sojojinta, rundinar soji tana da tsarinta na gudanar da aiki, ba ta tura dakarunta saboda banbancin addini ko kabila


Don haka rundinar tana gargadin Dr Ahmad Gumi da ya kama harcensa, ya dena yunkurin zubar mata da kima da mutunci, sanarwan ya fito ne daga kakakin rundinar sojin Nigeria Muhammad Yarima


Ikon Allah kenan, shikenan an mayar da Musulmin Arewa kaskantacce karamar danga dadin hayewa bai da 'yancin ya fito ya fadi gaskiya sai an kamashi ko an masa barazana


Tsawon shekaru akwai Malaman addini wadanda ba Musulmi ba,  babu irin maganganun karya da sharri domin su tayar da hankali da haddasa fadan addini da ba su fada ba a Nigeria,  ga irinsu nan su Femi Fani Kayode, TY Danjuma, Professor Jerry Gana da sauransu


A Shekarar 2018 su TY Danjuma da manyan jigajigan kungiyar addininsu har tattaki sukayi zuwa Kasar Amurka suka zauna tare da wani kwamitin sirrin tsaro na Amurka, sukace Gwamnatin Buhari da sojojinsa suna kashe mabiya addininsu


A farkon wannan shekarar,  shugaban darikar Katolika na jihar Sokoto Mathew Hassan Kukah har kira yayi ga sojojin da ba Musulmi ba su kifar da gwamnatin Buhari


Amma duk wadanda suke fadin irin wadannan maganganu ba a taba fitowa an kama sunayensu an gargade su ba, watakila saboda ba Musulmai bane, su kam suna da 'yanci da daraja, ana jin tsoron a tabasu saboda uwargijiyarsu Amurka da Isra'ila


Dr Ahmad Gumi tsohon soja ne, wadannan 'yan kuci ku bamu da suke mishi barazana da gargadi a yanzu duk ya rigasu shiga aikin soja, ya fisu ilmi da sanin sirrin tsaro, saboda ya karancin tsaro a boko da addini, barazanarsu ba zai tasiri a zuciyarshi ba


A raddin da Dr Ahmad Gumi ya mayarwa kungiyar mabiya addinin nasara, ai ya ambata sunayen kwamandojojin da suka yiwa fulani kisan kare dangi a jejin Birnin Gwari daga shekarar 2014 zuwa 2015, wadanda suka bada umarnin kisan ba Musulmi bane,  kuma yace su kaishi kotu ya kawo dalili idan sun isa


Muna tare da sabon jagoranci na rundinar sojin Nigeria, kuma zamu cigaba da baku dukkan goyon baya da gudunmawa don tsaron Kasarmu, amma fa idan aka biyo ta karkashin kasa akace za'a yaki Malamin Musulunci don ya fallasa asirin makiyan mu, to wallahi zamu raba hanya da ku


Yaa Allah Ka tsare mana Sheikh Dr Ahmad Gumi daga dukkan sharri da makirci Amin

 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments