Min menu

Pages

TONA ASIRIN ZINDIKI ABDULJABBAR KABARA

JANA'IZAR AƘIDAR 'YAN KOGON HALAKA, ZINDIƘI ABDULJABBAR ASIRINSA NACI GABA DA TONUWA!


 Kwararren Malamin Sunnah a fagen Qur'ani da Hadisi Malamin da ya kware sosai wajen fallasa asirin yahudawan duniya, wato Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya sake yin karatu zama na Huɗu mai taken JANA'IZAR AQIDAR 'YAN KOGO darasi na Huɗu (4) a jiya yaci gaba da tona asirin bakin bayahude na cikin gida Zindiqi kuma Mulhidi Munafukin Allah Abduljabbar Nasiru Kabara, Malam yayi masa Kwatsa-kwatsa Malam ya Zayyano wasu daga cikin miyagun lafuzzan da Zindiqi Abduljabbar yayi na zagin Manson Allah SAW da Sahabbansa  akwai cewar da yayi: 


1. Ya cewa Manzon Allah SAW  Mazinaci mai zina da mata a kan hanya.(Wal'itazubillahi) 😢


2. Wai Sayyidina Umar RA ya jefe Manzon Allah SAW da dabino saboda Manzon Allah SAW yayi masa Wa'azi.


3. Wai Abu Hurairah yayi tsirara a gaban Manzon Allah SAW a cikin Masallaci.


4. Kana da damar ka auri mata fiye da Huɗu.


5. Kuma yace Gawar Manzon Allah SAW ta ruɓe ta kumbura tayi wari bayan rasuwarsa.


Da irin waɗannan munanan lafuzan wannan Ja'irin mutumin yake jifar Manzon Allah SAW da Sahabbansa, idan anyi magana yace a littafan Sunnah ya gani, ku kalli wannan Muhadarah din ta Malam Bashir zaku gane shin a cikin waɗanne littafan shi zindiƙin yake ɗauko wadannan miyagun lafuzan na Ridda da Kafurci ya jinginawa Manzon Allah SAW da Sahabbansa.


Malam yace kada Zindiƙi yayi tsammanin ɗage Titsiyeshi da kotu tayi alheri ne a garesa shakka babu wannan zaman titsiyewar sai anyi shi.


Kada ku manta kuyi share kuma kuyi subscribe na channel dinmu AL-ESTIQAMAH TV  a YouTube domin samun karin ilmantarwa.


Allah Ya sakawa Malam da alheri, Yaa Allah Ya kare Musulunci da Musulmai daga miyagun akidun su Zindiƙi Abduljabbar Amin.


 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments