Min menu

Pages

Sun yiwa matar aure fyade tare da tilasta mijinta ya tsaya ya gani

Mutane hudun da aka kama da laifin yiwa wata matar aure fyade sannan sun tilastawa mijinta ya tsaya ya gani.
An yankewa mutane hudun da sukaiwa matar aure fyade tare da tilasta mijinta ya tsaya ya kalla hukuncin kisa ta hanyar rataya.


Wannan lamarin ya faru ne a kasar Iran inda mutane hudun suka hau saman har gurin da miji da matar suke domin suyi musu fashi daga karshe suka bige da yiwa matar fyade tare da tilasta mijinta ya tsaya ya gani.


Inda suka hada hannu da kafar mijin suka daure tare da tursasa shi kallon abin tsiyar da sukewa matarsa.


Bayan an tsawaita bincike an gano mutanen da suka aikata wannan mummunan aikin wanda daga karshe aka kama su.


Kotun saurara karar laifin ta tura mutanen babbar kotu inda acan aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.


Ku sani kasar Iran tana daya daga cikin manyan kasashe wanda suka tsani aikata laifin fyade.

Comments