Min menu

Pages

Sun kone wani dan sanda da ransa

 Wasu fusatattun yan daba sun yiwa wani dan sanda kisan wulakanci ta hanyar kone shi da ransa.Al'amarin ya faru ne a jihar akwa ibom inda yan daban suka je har gida suka kashe dan sandan.


Saidai majiya tace wannan ba shine karo na farko ba da ake kashe yan sandan ba a jihar.


Kusan shine karo na biyu da al'amarin yake faruwa a kan yan sandan.


Wannan abin daya faru ya tsorata mafiya yawa daga cikin mutanen musamman wanda suke zaune a jihar.


Domin a cewarsu hankalin su baya kwanciya kuma bazai kwanta ba idan har za ana kashe jami'an tsaro to su fararen hula ya kenan za suyi?


Dan haka suka nemi gwamnati data sanya ido sosai domin tabbatar da tsaro

Comments