Min menu

Pages

An gano wani gida da ake sato yan mata ayi musu ciki domin su haihu ai wa jariran haka

 Wani gida da ake sato yan mata kuma ayi musu ciki domin su haihu a dauke jaririn..An gano wani gida da ake daukar yan mata domin a kwanta dasu domin suyi ciki su haifu domin a dauki jaririn ayi wani abu dashi.


Rundunar yan sanda itace tai nasarar gano wannan gidan, saidai bayan wannan aikin da ake aikatawa cikin gidan an gano har shaye shaye ake a gidan a takaice dai mashaya ce.


To amma batar da kama kawai akai aka nuna gidan a matsayin gidan shaye shaye wanda mata masu zaman kansu ke zuwa, to ashe ciki kawai aka tara mata ana musu domin su haihu a sayar da jaririn.


Gidan yana cikin garin Nnewi dake jihar Anambra.


Bataliyar yan sandan tace tayi nasarar kamo wasu mata har guda hudu a gidan da suke dauke da ciki wanda ake zaman jiran su haihu kuma a sayar da jariran.


Shugaban yan sandan yace wannan kayan shaye shayen da ake sayarwa a gidan kawai bada kafa ne domin a kawar da hankalin mutane daga mummunan aikin da ake cikin gidan.


Matar da take da gidan bata da aiki sai kawo yan mata domin ayi musu ciki idan sun haihu kawai sai a sayar da abinda suka haifa.


To yanzu dai yan sandan sun baza komarsu wajen neman wannan matar domin a hukunta ta to amma tayi layar zana.

Comments