Min menu

Pages

 

 KAZA ME SHINKAFA

¤Kaza

¤Shinkafa

¤Bota

¤Curry

¤Green pies

¤Karas

¤Cabbage

¤Pies

¤Kayan miya

¤Zare da allura

¤Mai

Kisami shinkafarki da kika fara dafawa tayi rabin dahuwa,wato da garas garas dinta ki zuba a kwano kiyanka green pies da karas da cabbage, kizuba pies kiyanka attarugu da dafaffen kwai ki zuba maggi, curry, gishiri,kizuba man gyada kadan 



kijuya shinkafan da wannan kayan da kika zuba. to dama kin wanke kazarki kin cire kai da kafa da kayan ciki kinshafe Kazan da maggi da kayan kamshi,da attaruhu da kika jajjaga da curry, sannan ki shafebayanta da bota,



kizuba shinkafar da kika hada a cikin kazar sai ki Sa zare da allura ki dinke cikin kazar amma allura sabuwa zaren ma sabo. Idan kin dinke sai kisa a oven ki gasa



   WAINAR GERO

Kayan Hadi:

Gero (hatsi) gwangwani 4

Karkashi cokali 3

Kanwa

Suga Yadda kike so

Yadda Akeyi:

Zaki bayar a surfo miki geronki ki wankeshi ki gyara ma ana ki regeshi ko yana da tsakuwa sai ki bayar amarkado miki karkisa masa komai, idan an markado sai ki ajeshi waje me dumi, amma dake yanzu lokacin sanyine sai ki sa masa yeast 



idan gwangwani 4 ne sai kisa masa yeast karamin cokali daya,sai ki jika karkashin shima ki zuba, idan kuma ki gwanace wajan iya sarrafa karkashi to ba matsala zaki iya zubashi ba sai kin jikashi da ruwaba sai ki dinga juyawa zakiga yana dada yin kauri da danko sai ki aje zuwa lokacin da zaki soya,



 idan kinzo suya dama kin jika yar kanwarki saboda tsamin kullu sai ki dan sakata tare da suga yadda kikeso sai ki dinga diba kina soyawa shikenan za’a iyacinta da farfesun kan rago ko kuma miyar da ta dace.



     DOUGHNUTS


Ingredients;

*3 & half cup flour

*1 tbspn yeast

*1 tbspn powdered milk

*1/2 cup sugar

*2 tbspn butter

*1 egg

*Water as required



 -Zaki tankade flour a rubber me kyau kisa yeast,milk,sugar and egg ki juya


-Zaki rika zuba ruwa a hankali kina juyawa(kar yayi ruwa kar Kuma yacika tauri)har yahade sannan kiyta murza shi har na tsahon mintuna 5


-Sannan kisa butter kici gaba da murzawa har tsahon mintuna 30 yayi laushi


-zaki raba dough din ki murza shi kisa doughnut cutter ki fidda shape(in bakida zakiy amfani da cup da murfin jarka)


-Ki barbada flour a tray ki rika jerasu har kigama


-Zaki rufe doughnuts dinki tsahon 40 minutes waje me dumi har su tashi


-kisa mai awuta har yyi zafi,wutar kasa  kisoya har yayi golden brown


         CHICKEN WRAP

ingredients:

2 cups of flour

3/4 water

1 tsp salt

1 tsp sugar

3 tbspn veg oil


For filling

shredded chicken

scotch bonnet

onions

green pepper

ginger powder

garlic powder

curry

onga

seasoning

spices

cabbage

carrot

cocumber

mayo

ketchup

powdered milk( optional)

sugar( optional)


steps::


dafarko zakiyi making dough Dinki ki ajiye a gefe....


    ki zuba veg oil a pan kikawo diced onion da grated scotch bonnet kizuba ki juya kikawo shredded chicken kizuba kizuba kikawo green pepper Wanda kikayanka kizuba kikawo ginger and garlic powder,


 onga, seasoning, curry,spices kadan kizuba kijuya kibarsu su hade jikinsu sekisauke ki ajiye a gefe...ki dauko dough Dinki ki rabashi into 5-6 pieces kidauki daya daga ciki kiyi rolling dinshi ki Dora nonstick pan ki gasashi both side seki cire ki ajiye a gefe ki rufe... kidauki ketchup da mayonnaise



 kizuba a bowl kizuba powdered milk half tbspn depending kizuba sugar kadan ki juya sekidauko shawarma bread Dinki ki shafa akai kidauko cabbage kizuba kidauko grated carrots kizuba a gefen cabbage din sekizuba cocumber kikawo hadin chicken Dinki kizuba seki nade kamar kina nade tabarma haka zakiyi harkigama..serve and enjoying


Comments