Min menu

Pages

ABAR ABDULJABBAR KABARA YACI GABA DA KARATUNSA CEWAR MAJALISAR MALAMAN KANO

Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya Ta bukaci Ganduje Ya dage Takunkumin da Ya Sakawa Sheikh Abduljabbar 


Majalisar Malaman Addinin Musulunci a Najeriya ta nemi Gwamna Abdullahi Ganduje da ya sassautawa Sheikh Abduljabbar Kabara - Kungiyar ta bukaci da ya sake bude masallacin Shehin Malamin domin gudanar da ayyukansa na yau da kullun - Ta ce hakan ne zai zamo adalci kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ta ba kowani dan kasa yancin yin addininsa Majalisar Malamai ta Najeriya, karkashin inuwar kungiyar Malaman Addinin Musulunci a Najeriya ta yi kira ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje. 


Ta nemi da ya dage takunkumin da ya sanya wa malamin nan, Sheikh Abduljabbar Kabara tare da sake bude masallacinsa domin gudanar da ayyukansa na yau da kullun, Vanguard ta ruwaito. Ku tuna cewa a watan da ya gabata, Ganduje ya hana Abduljabbar yin wa’azi da gabatar da Sallah a masallacinsa sakamakon zarge-zargen da wasu malaman addinin Islama ke yi a jihar. 


 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments