Min menu

Pages

Girkinmu na yau kunun Alkama ne, da fried rice, sai meat sauce da kuma Alala nd stew.


    kunu da garin alkama

alkama

madara

sugar

ruwa


Uwar gida da farko bayan an barza miki alkama, saiki debo garin a cup daidai yadda kike bukata sai kisa a ruwan zafi kina juyawa har yayi kaurin da kike so kafin ki sauke inkin sauke saiki sa madara da sugar a ciki. A sha lafia.


Note 

barkanmu da sake saduwa daku a wannan fili namu na girke-girke uwar gida da fatan ana cikin koshin lpy yaya zafi ayau nakawo muku yadda ake kunun alkama, kunun alkama yana da matukar mahimmanci a rayuwar dan adam. bayan ga kasancewarsa abin sha, anyi ittikafin yana kara kuzari da sanya nishadi ga dan adam sabida sunadaran da ya kunsa..masana sun bayyana cewa kunun alkama yana da alfanu ga ma'aurata kuma abin sha ne dayake rike ciki fiye da kokon gero ko na masara


Note 2

za a iya sha haka bayan an zuba madara da sugar. za a iya ba yara da jarirai a matsayin abin da zai kara musu kuzari da Lafiya.    ALALA WITH STEW

Ingredients

Wake 

Tattasai

Attaruhu

Albasa

Spices

Kayan dandano

Man ja 

Kwai 

Kifi 

Dafarko zaki jika wakenki yajiku sannan ki murje da hannun ki inkuma kinga dama zaki iya Kai barji sannan kijika sai ki wanke shi yafita sosai Sannan ki zuba tattasai attaruhu albasa. A markada shi kar ki cika mai ruwa madaidaici sai kizuba kayan dandanonki dama kin dafa kwanki da kifinki sai ki zuba da manja da yar albasa sai ki daura saiki dauko tukunya ki zuba ruwa madaidaici saiki zuba shikenan idan ya dahu sai ki ci da stew ko dayaji         FRIED RICE

  Ingredients

White rice

Carrot

Peas

Greenbeans

Onion

Attarugu 

Garlic/Ginger

Sweet paper

 For the spices 

 Bayleaves 

   Method

Zaki dafa shinkafarki fara amma karta dahu sosai kuma kartayi tauri sai ki ajiyeta agefe. Sai ki dauko veggies dinki ki gyara ki wanke saiki yanka su yadda kikeso, sai ki jajjaga attaruhu da tafarnuwa ki juye a tukunyarkikisa mai yafara soyuwa sai ki juye veggies dinki kici gaba da soya sai ki dauko maggie da dan gishiri kisa kisa curry idan yakusa sai ki juye wannan fara shinkafar ki cigaba da soyawa idan komai yabi jikinta saiki dauko ruwan kazarki ko nama ludayi daya kisa koran tattasai,bayleaves da dandano saiki juya ki tabbatar komai daidai sai ki rage wutar tayi kasa kibata 15min
         Meat sauce

Ingredients

Attarugu

Albasa

Tafarnuwa

Maggie/salt

Spices

Curry

   Method

Zaki gyara namanki ki yanka yadda kikeso sai ki wanke ki tafasa ki soya, saiki ajiye shi agefe. Sai ki gyara attarugu,albasa da tafarnuwa ki jajjaga sai dauko namanki sai ki zuba wannan jajjagen akai ki dora awuta Sai kisa mai da gishiri kidan soya samasama saikisa ruwa bamai yawaba kisa maggie,spices da curry sai ki barshi ya dahu amma da dan ruwa ake barinshi zakiga yayi kyau

Comments