Min menu

Pages

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yayiwa gwamnati alkawari ku karanta kuji

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yayi wa gwamnatin wani alkawari wanda muke fatan abin ya tabbata Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yayiwa gwamnati alkawarin zai tallafa mata wajen magance matsalar tsaro


Malamin da yayi fice wajen zama ko kuma shiga jeji domin yin sulhu da kuma wa'azi tare da nasiha ga yan bindinga yayiwa gwamnatin Nigeria alkawarin taimakawa wajen shawo kan matsalar tsaro data addabi kasar nan musamman yankin arewa.


Malamin yace Insha Allahu zaiyi bakin kokarinsa wajen taimakawa gwargwadon yinsa dan ganin an samu masalaha na tabarbarewar tsaron daya addabi kasar.


Me bada shawara kan yanayin tsaro Baba gana munguno  shine ya fitar da sanarwar cewa sun zauna da shehin malamin kuma yayi musu wannan alkawarin.


 A wata tattaunawa da sukai da manema labarai ranar alhamis yace sunyi wannan maganar lalle shida malamin.


Dan haka muna jira muga ta yadda Malamin zai taimaka wajen shawo kan wannnan matsalar ta tsaron a cewarsa.


Matsalar ta'addanci da rashin tsaro ita ce ta addabi kasar nan tsawon lokaci wanda mutane keta fatan gwamnati su shawo kanta.


Comments