Min menu

Pages

MATSALAR TSARO A NIGERIA YA YI MUNI LAIFIN NA WAYE?


 MATSALAR TSARO A NIGERIA YA YI MUNI LAIFIN NA WAYE?


Lalacewar tsaron kasar nan abin ya wuce duk yadda mutane suke tsammani kowa ya shiga rudu shugabannin sai fagam fagam suke yi su Kansu hanyar ta qulle musu


Mutanen sabon birni na jihar sokoto suna cikin tashin hankali wasu mutane "Yan ta'addah sun addabe su suna yi musu rashin mutunci da rana tsaka a cikin kasuwa suke kama mata su yi musu fyade ba Wanda ya isa ya hana su


Haka manoma basu isa su yi noma ba sai sun biya haraji sannan duk abin da ka noma sai ka warewa " Yan ta'adda nasu kason suna kashe mutane suna dauke mutane su tafi dasu jeji sai an basu kudi sannan su sake su


Mutanen yankin gani suke yi kamar ba'a Nigeria suke ba ko kuma babu hukuma domin Gwamnati ta gaza kare su a wannan yankin ana yin ta'annatin da an Dade ba'a keta alfarmar Dan Adam kamar Wanda ake yi a yankin sabon birni ba duk wani nau'in ta'addanci ba Wanda ba'ayi a yankin sabon birni


Ga katsina da zamfara da kebbi da Kaduna da jihar Niger "Yan ta'addar jeji sun gallabe su ga boko Haram ta na ta kai hare hare suna kashe mutane suna sace mutane har da sojoji


Ga shugaban kasa ga Gwamnoni ga soja ga sauran jami'an tsaro duk muna da su amma abin kullum sai qaruwa ya ke yi


Shin wannan Matsalar Laifin na waye ne wacce hanya za'abi don shawo kan wannan ta'addancin Jami'an tsaro ne basa yin aikin su ko kuwa jama'ah ne basa ba wa jami'an tsaro hadin kai?


Ina kira ga shugabanni suji tsoron Allah su yi abin da ya dace a wannan matsalar ta tsaro domin za su zama abin tambaya a gaban Allah a Ranar Lahira mutanen Nigeria suna cikin tashin hankali suna neman ceto


Sannan ina kira ga "Yan uwa mu cigaba da yin addu'ah da neman gafara gurin Allah ko zai tausaya mana ya bamu kwanciyar hankali da salama


Allah mun tubu muna roqonka ka ji kan mu ka dawo mana da aminci da kwnaciyar hankali ka ya ye mana damuwar mu ka shiryi wadan nan "Yan ta'addar.Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments