Min menu

Pages

Maulud din sokoto yan bindinga sun sace mutane hamsin a hanyar zuwa saidai ashirin daga cikinsu...

 Yan bindiga sun tafi da mutane hamsin akan hanyar zuwa gurin maulud na sokoto saidai ashirin daga cikin mutanen..Yan bindigar sunyi awun gaba da mutane kimanin guda hamsin akan hanyar tafiya gurin maulud yau da za'a gabatar a jihar sokoto.


Kamarin ya faru ne a jihar Katsina kan hanyar kankara zuwa scheme a ranar alhamis da dare 


Wata majiya mai karfi tace anyi awun gaba da mutanen ne tun da daren alhamis akan hanyarsu ta zuwa maulud jihar sokoto.


Da farko mutane hamsin yan bindingar suka sace amma daga bisani guda ashirin sun tsere inji masu bada labarin.


Yanayin tsaro a kasar nan sai sake tabarbarewa yake yadda ko ina in mutum zaije za kaga hankalinsa bai kwanta ba saboda tunanin abinda zai iya kaiwa ya kawo 

Comments