Min menu

Pages

Al'ummar kasar Tanzania sun fashe da kuka lokacin da za'a fice da gawar shugaban kasar su.

Cikin jimami talakawa dama yawancin yan kasar Tanzania sun fashe da kuka lokacin da aka zo ficewa da gawar shugaban kasar su daya rasu.Abinda ya faru ya jawo maganganu da yawa a kasashe da dama ciki harda Nijeriya da Nijar.

Mutane na danganta kukan da yan kasar suke bayan ganin za a fice da gawar shugaban kasar nasu baya rasa nasaba da tsananin kaunar da suke masa.

Wasu kuma suna ganin tsananin kyautata musu da yake ne yasa talakawa suke kaunarsa.A kwanan baya ne dai shugaban kasar Tanzania ya rasu harma aka bayyana mataimakiyarsa ce zata gaje shi.

To saidai anyi ta maganganu da akaga yadda yan kasar suke ta famar rusa kuka tun lokacinda aka fito da gawar ta shugaban kasar.

Comments