Min menu

Pages

Da dumi-duminsa:- An sako daliban makarantar Jangebe da aka sace

An sako daliban da aka sace na jangebeGwamnatin jihar zamfara ta tabbatar da sakin yan matan makarantar Jangebe.

A wata shira da BBC Hausa tayi da gwamnan jahar Bello matawalle da safiyar ranar 2 ga watan maris,gwamnan yace an sako daliban guda 279 da aka sace, yanzu sun sami iskar yanci.

A lokacin da ake shira da gwamnan ta BBC yace daman dalibai 279 suka sace kuma duka sun sakosu cikin koshin lafiya ba tare da bayar da wani kudin fansa ba, ya kuma kara da cewa kawai anyi tattaunawa ne da yan fashin dajin kafin a sako daliban.

Matawalle ya kara da cewa: "Alhamdulillahi yanzu ma haka ga yaran nan muna karbarsu ni damai dakina suna shiga gidan gwamnati haka kuma gani ga tawagar da suka amso yaran cikin koshin lafiya".

A ranar juma'a ne dai 26 ga fabarairu aka tashi da sabon tashin hankali a jangebe dake jihar zamfara dangane da sace dalibai da wasu yan bindiga sukayi.

Wannan dai na zaman  daya daga cikin manyan garkuwa da mutane da akayi a arewa maso yammacin Najeriya, wannan al'amari dai ya zama tamkar wani wasan kwaikwayo ta yadda ake sace daliban kuma bayan an dawo dasu a kwashi wasu.

Dangane da wannan al'amari ko wane mataki gwamnatin Najeriya zata dauka domin kada a sake sace wasu daliban?

Comments