Min menu

Pages

Jahohi goma da sukafi kazanta a Nijeriya

 Jerin wasu jahohin guda goma da suka fi kazanta a Nijeriya.Kowa na bukatar zama ko rayuwa a guri mai kyau tare da tsafta domin jin dadi da kuma gujewa kamuwa daga cututtuka.


Sannan babu mai son rayuwa cikin kazanta ko rashin tsafta ko kadan.


Nijeriya kasace da take da girma kuma ta tara jahohi masu yawa, wanda hakan yasa dole za a samu jahohin da suke da tsafta ko akasin haka ma'ana kazanta.


A yau muna dauke da jerin wasu jahohi har guda goma da alkaluma suka nuna sunfi kowacce jiha kazanta a Nijeriya.


√ Lagos jihar Lagos kusan yanzu tana daga cikin jerin manyan jahohin da suka fi kazanta a Nijeriya duba da yanayin yawan mutanen da jihar take dashi, sannan koda yaushe guraren akwai ruwa.


Mafiya yawa mazauna lagos sukan zubar da wasu datti ko kayan kazanta a gefen titi dadai sauransu.

Ada ba haka jihar take ba amma yanzu saboda babu gyara ko tsawatarwa abubuwa sun canja.


√ Anambra Jihar Anambra itama wata jiha ce mai yawan kazanta da tara datti wanda take bukatar ayi mata aiki gaskiya domin a maida ita mai tsafta.


Dan Allah ka ziyarci  daya daga cikin manyan birnin jihar kamar Onisha zakasha mamaki domin za kaga shara da sauran karukuce zube akan titina suna wari ba tare da an debe ko an gyara gurin ba.


√ Abia shima guri ne mai tarin kazanta wanda tasa jihar take da wuyar zama saboda karancin tsafta da suke fama da ita.


√ Kaduna jihar kaduna ma na daga cikin jihohin da aka nuna suna fama da matsalar kazanta saidai bawai cikin garin kadunan bane keda wannan matsalar sauran garuruwan dake zagaye dasu ne keda wannan matsalar.


√ Ogun mutane za suyi mamaki idan aka lissafa jihar Ogun cikin jahohin masu kazanta wannan na zuwa ne saboda karancin guri da jihar ke fama dashi.


√ Kano Wata jihar ma dake fama da kazantar kenan itace jihar kano duk kuwa da cewa jihar tana daya daga cikin jihohin Nijeriya masu arziki da tarin abubuwa, dan haka in fito ina fada muku gurare masu kazanta cikinta wani abu ne amma ga masu zuwa jihar zasu fadi gurare masu yawa dake da kazantar.

√ Oyo jihar itama tana fama da matsalar rashin tsafta.

√ Jigawa duk da kasancewar jihar ba a tare take guri guda ba amma akwai wasu daga cikin manyan biranen cikinta da suke da kazanta kodan saboda taruwar ruwa dadai sauransu

√ Zamfara itama ta biyu sahun jerin jahohi masu fama da kazanta kamar yadda binciken ya nuna.

Daga karshe bawai mutanen dake jihar bane kazamai kawai yanayin gurin ne dan haka dan Allah ana yi mana hakuri idan mun fadi wasu abubuwa da basu yi muku dadi ba bincike ne yazo da haka.
Comments