Min menu

Pages

Buhari yace zai taimakawa janhuriyar Nijar wajen yaki da yan boko haram

 Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari yace zai taimakawa janhuriyar Nijar wajen yaki da yan boko haram.Sannan zai sake taimaka Nijar wajen yaki da yan ta'adda masu tada kayar baya.


Shugaban kasar Muhammadu Buhari yace a shirye Nijeriya take ganin ta tallafawa nijar dama sauran kasashe dake fama da matsalar yan boko haram da kuma yan ta'adda.


Wanda yake magana da yawun shugaban kasar a media Garba shehu shine yai wannan maganar ranar talata.


Garba shehun yace Buhari da Muhammadu yousuf shugaban kasar nijar sun cimma matsaya akan zasu karfafa tsaro tsakanin kasashen dan ganin an kawar da yan boko haram din da suka damu mutane.


Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa bisa ga kisan mutane dari da talatin da bakwai din da akayi a Nijar.


Yace yana jajantawa iyalan mutanen da aka kashe a wannan harin da aka kai.


Sannan yace dole sai an tashi tsaye wajen yaki da yan ta'addan dan haka a shirye kasar Nijeriya take domin ta taimakawa janhuriyar Nijar din.

Comments

1 comment
Post a Comment

Post a Comment