Min menu

Pages

Darikar Tijjaniyya Ta Musanta Nada Tsohon Sarkin Kano Sanusi Khalifan Tijjaniyya Na Nijeriya.


 BAYA DA KURA: Darikar Tijjaniyya Ta Musanta Nada Tsohon Sarkin Kano Sanusi Khalifan Tijjaniyya Na Nijeriya.


Sheikh Mahi Nyass, shugaban darikar Tijjaniya na duniya wanda ake kira da Khalifatum Arrm, ya bayyana hakan yayin da yayi jawabi ga manema labarai a Sokoto.


Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa, Nyass, wanda shine da kuma magajin Shehu Ibrahim Nyass, yace in har za a yi nadi ana tantancewa sannan a zaba daga cikin mabiyanta na Najeriya da Senegal.


Irin wadannan hukunci ana tattaunawa ne sannan a amince kafin a sanar. Bayan an zaba mutum, akwai wasikar amincewa daga malamai wacce Khalifatul Arrm zai saka hannu kuma ya mika ga wanda aka nada,” Nyass ya ce.


Ya ce Sanusi bai nuna bukatar kujerar ba kuma shugabannin basu riga sun fitar da tsarin da za a bi ba wurin wannan nadin.


“Hadin kan ‘yan kungiya yana da amfani kuma ina kira ga kungiyar da ta mayar da hankali wurin bauta, kara dankon zumunci da kaunar juna,” ya ce.


Sheikh Ibrahim Dahiru-Bauchi, da ga fitaccen malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kwatanta labarin nadin Sanusi da labarin bogi.

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments