Min menu

Pages

Dalilin mu na cewa baza muyi mukabala da Abduljabar ba inji Dahiru Bauchi

 Bamu amince a zauna muqabula da Abduljabar ba inji Dahiru Bauchi saboda wannan dalilan..Shehun Malamin nan na kungiyar darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Bauchi yace mun goyi bayan a rushe makarantar yaron nan Abduljabar tare da masallacin sa sannan a hanashi yin wannan abin da yake cewa karatu amma bamu goyi bayan a zauna muqabula dashi ba.


Malamin yace yin zama dashi tamkar dawo da abinda ya faru a farko ne ma,ana zai sake fadar wadannan maganganun masu muni akan ma'aiki wanda hakan ba dacewa bace.


Malamin yace bai kamata a maimaita sabo ba domin da zarar an aminta da zaman to yaron zai maimata kalamansa masu muni wanda mu kuma hakane bamu so.


Yace wannan yaron ko kadan bai fahimci hadisan da yake kawowa fassararsu ba asalima gurguwar fahimta yai musu.


In masu sauraro basu manta ba a kwanan baya Abduljabar ya fito yayi wasu furuci marasa dadi akan sahabban manzon Allah wanda hakan bai yiwa mutane da yawa dadi ba wannan yasa gwamnatin Kano ta dakatar dashi daga karatun da yake.


Saidai shi Abduljabar din ya fito ya nuna cewar ba'a kyauta masa ba hakan yasa gwamnatin kano din ta saka zaman mukabalar tsakansa da manyan malamai domin a zauna to saidai abin har yanzu bai iyu ba.

Wanda wannan rashin zaman bai yiwa da yawa dadi ba.

Comments