Min menu

Pages

Bakar Guguwa 1 



Labari ne mai tsananin dadi da debe kewa

Zuhairu yana tafe akan ingarman dokinsa cikin sassarfa da hanzari, ya nufn bakin wani makeken lambu ma'abocin ni'ima ta 'ya'yan it'atuwa furanni da koramu masu gudanarwa a cikinsa. 


Zuhairu jarumi ne na gasken gaske wanda jarumta da bajintarsa ta shahara a dukka nin fadin alkaryun dake kusa da brinin su, yana da karfin zuciya da rashin tsoro na ban mamaki. Shi kadai yakan fasa rundunar mahara da masu tare hanya suyi fatake masu tafiya a daji fashi. 


Al'addar Zuhairu ce yakan ziyarci bakin wannan lambu ako wane yammaci dan yaga wata 'yar sarki da ke zuwa lambun tare da kuyangunta ako wace rana. 


Tun daga ranar da ya fara ganinta cikin wasu ranaku da yake yawo a wannan waje, ya ji zuciyarsa takamu da tsananin begenta, irin wanda bazai musaltu ba, sai dai baisan makomar rayuwarsa ba. bisa ga kaunar da yake yiwa wannan 'yar sarki, kasancewarta mai girma da daraja daraja cikin man'yan 'ya'yan sarakunan duniya. ° 


Ya yi sani da cewa 'ya'yan sarakuna a wannan lokaci' basa auran wanda ba dan sarki kamar su ba. Ko kuma attajiri wanda dukiyarsa ta shahara. Shi kuma gashi ba d‘an sarki ba, dan haka ya kauda kai gabarin tunkararta ya bayyana mata abinda yake zuciyarsa, na daga begenta saboda girman matsayinta da ya wuce nasa. Sai dai yakan ziyarci bakin wannan lambu da take zuwa akowanne yammaci dan ya ganta. 


Da isarsa bakin wannan lambun ya sauka daga kan dokinsa ya kaishi gefe ya daure. sannan ya koma gindin wata itaciya dake fuskantar kofar lambun ya zauna ya 


dauko wata Sarewa ta azurfa da ya gada a wajen

mahaifinsa ya Soma busawa cikin nishadi yana mai

sauraran isowar wannan 'yar sarki dan ya ganta.

Zuhairu yana zaune a wannan waje har rana ta kusa

faduwa wannan yar sarki bata zoba, ransa ya baci

saboda kewar rashin ganinta ya yi shiru yana tunani da

sake-sake a ransa.

Yana cikin wannan hali kamar daga sama sai yaji

anyi masa magana dawata irin zazzakar murya mai

sanyi daga ababan sauraro. Muryar tace dashi.

"Da kazama mai yiwa zuciyarka adalci da babu

shakka da ka rabu da begen wadda bata san kana

begenta ba. Da ka rabu da tunanin wadda bata san kana

tunaninta ba, da ka sauya lamarinka daga kuncin kaunar

wadda baza ta soka ba, saboda girman matsayinta da ya

wuce naka."

Zuhairu ya dago kansa cikin sauri ya dubi inda ya ji

muryar da ta yi masa magana amma baiga kowa ba, ya

duba kowane bangare na daga inda yake baiga mai

maganar ba.

Muryar ta sake cewa da shi "kada ka damu ko kaji

tsoro mai kaunarka ce take yin magana da ka, ko kana

inkarin abinda na ambata na bayyana gare ka dan

tabbatarwa."

Zuhairu ya dubi inda ya kejin muryar ya ce "ldan kin

kasance tare da alhairi ki bayyana gare ni don nasan wacece ke da kuma dalilin zuwanki gareni har ki kayi sani da halin da nake ciki da fadar Magana mafi munin ambato, 1dan kuma bakya tare da alhairi to kuwa ina mai neman tsari dake tare da rokon kinisanta dani ko waccce ke

Zuhairu ya ji anyi dariya cikin tattausar murya.

sannan muryar ta ce dashi "Zan kasance alhairi gareka tunda ina tare da dumbin kaunarka a zuciyata, dan haka zan bayyana gareka nasanar dakai koni wacece da kuma abinda ya kawoni gare ka kamar yadda ka ce."


Ana gama fadar maganar sai yaga wani farin haske ya bayyana a gabansa daga cikinn farin hasken sai ga wata mace ta bayyana kyakkyawar budurwa tana sanye da fararan tufafi hannunta rike da wani dan karamin

gora abin zagayewa da gura ye da kambuna irin na aikin sihiri. 


Ta dubeshi tayi murmushi tare da juya fararan

idanunta dan jan hankali. Zuhairu ya kare mata kallo sannan ya ce da ita "Wacece ke kuma meya kawoki gareni cikin wannan

yanayi na aikin sihiri, ki sani cewa babu aminci tsakaniin Musulmi da duk wasu mushiriki ma'abota tsafi da sihiri, matukar basu tuba sunbi Allah ba." Kyakkyawar budurwan nan tayi dariya sannan ta ce da shi "Da dai kayi sani da irin martaba da daraja da

take tattare da alkaluman sihiri, da kuwa kayi biyayya ga ma'abota mallakarsu dan kazamo daga cikinsu. Shine

abin tunkaho da alfaharin mu dan a yanzu duniyar

ma'abota sani na alkaluman sihiri ne keda tasiri akan

komai."

Ta sake yi masa murmushi irin na jan hankali sannan

ta ci gaba da cewa "Suna na BUNIYATUL HAJARI BIN KAUWAS mahaifina shine shugaban bokaye da

ma'abota aikin sihiri dake yammacin bimin SINAR. Ya

rasu cikin wannan shekarar yana tsakiyar tafiya ba tare

da wata rashin lafiya ko cuta ba, bayan rasuwar sane

muka gaji sirrin tsafi da sihirinsa ni da yayana da ya rasu

ya barmu a duniya, na gaji kashi daya cikin dari na

alkaluman sihiri. Mahaifina yayana kuma ya gaji kashi

casa'in da tara daga ciki.

Dalilin zuwa na gareka kuwa shine na kasance mai

bibiyar rayuwarka tun daga lokacin da na fara ganinka

zaune a wannan waje kana busa sarewa, tun daga

busar sarewar da kake yi mai sanyaya zuciya har

wannan rana nakan ziyarci wannan waje dan na saurari

zuciyata ta kamu da tsananin begenka. Sai dai bantaba

bayyana gareka ka ganniba sai a yau, kuma na lura cewa

zuciyarka ta kamu da kaunar wata 'yarsarki da take

zuwa wannan lambu, dan haka na baiyyana gareka dan

na raba tunaninka da begen wadda bata san kana

begenta ba."

Zuhairu ya fusata dajin wannan magana ya ce da ita

"Da kinsan yadda nake tsananin gaba da kiyayyar

mushirikai ma'abota tsafi da sihiri da ko kusa baki

tunkari inda nake da bukatar na kaunace ki ba, kiyi

alkawarin zaki musulunta dan samun cabo da kaucewa

bata na aikin sihiri da kike aikatawa, ko kuma ki nisanta

da inda nake. Idan ba haka ba kuwa na rantse da wanda

raina yake hannunsa sai na halakaki da kisa mafi muni

da azabar kaifin takobina."

Buniyatu tayi dariya sannan ta ce da shi "Babu

kiyayya ko gaba a tsakanina da kai masoyina, idan da

ina gaba da kai zai zama mafi sauki gareni na halakaka

ta hanyar karfin tsafi da sihirina." Ta daga kurtun sihirn

da yake hannunta ta girgiza shi ta soma wasu irin surutai

da sambatu irinna aikin sihiri nan take wuta takama daga

kowace kusurwa hudu dake zagaye da Zuhairu. Sannan

wutar ta taso kansa gadan-gadan zata konashi  ya halaka

Zuhairu yayi niyyar Kaucewa amma yaji ya kasa

koda motsi daga inda yake kamar wanda kasa tarikeshi

Wutar ta taso masa haikan zata koneshi ya halaka sai da

ta kusa zuwa inda yake ya soma jin zafin da hucinta,

sannan sai yaga wutar ta mutu ta kuma bace ya dena

ganinta.

Buniyatu ta sake bushewa da dariya sannan ta ce da

shi "Wannan kadan kenan daga tasirin tsafi da sihirin

da na gada a wajen mahaifina wanda zan iya halakaka

dashi idan naso. Sai dai bani da nufin cutar da kai bare

aje ga batun halakaka, saboda kaunar da nake yi maka.

Kai dai kayi azama ga zurfafa tunani dan amincewa da

kaunar mai kaunarka, zai zama mafi kyautuwa gareka

ka

ka amince da bukatata muyi aure. Wannan shine

kudirina akanka kayi tunani akan maganar. Na barka

lafiya."

Tana gama ladar maganar sai yaga ta bace daga wajen

ya dena ganinta. Sannan yaji shuru bata sake yin magana

ba bare motsinta. Dan haka ya tabbatar da cewa ta tafi

tabar wajan, da ganan ya tashi ya kama dokinsa ya hau

ya nufi hanyar komawa gida.

Da isar Zuhairu gida ya daure dokinsa ya tafi wajan

kakansa MARWAN BIN HADIS wanda shi kadaine ya

rage masa a duniya. lyayansa sun rasu tun yana karami,

a hannun kakan nasa ya taso. Ya zauna kusa da shi ya

gaisheshi sannan ya kwashe labarin abinda ya faru

gareshi tsakaninsa da wannan shu'umar mace da suka

hadu da ita a fitarsa ta wannan yammaci, ya sanar da

shi.

Dattijo Marwan ya cika da mamakin wannan labari

sannan ya ce da Zuhairu "Babu shakka duniya ta kara

kazanta da shu'uman mutane mushirikai ma'abota tsafi

da sihiri a doron kasa."

Ya tashi daga inda yakezaune ya nufi wata akwatin

bakin Karfe dake karshan dakin ya bude, ya bincika

kasan akwatin ya dauko wani zobe na azurfa ya dawo ya

bawa Zuhairu sannan ya ce da shi "Ka sanya wannan

Zoben a dan yatsanka cikin yardar Allah zai zama kariya

gareka daga sharrin ma'abota tsafi da sihiri, babu wani

aikin sihiri da zaiyi tasiri akanka kuma komai rintsi kada

ka sake ka cireshi daga hannunka, a duk sanda wani

matsafi ya tunkareka ko mai aikin sihiri zakaji zoben

yayi mosti a hannunka koda kuwa baka ganinsa, haka

kuma idan kaji dokinka yayi haniniya to ka lura akwai

Wani abin cutarwa kusa da kai, dan shi yana ganin

abinda kai baka gani, kuma kada kasake kashiga inda

dokinka yayi gardamar shiga, haka kuma kada kaji

tsoron duk abinda dokinka baiji tsoron ganinsa ba. Kada

kamanta yawan addu'a aduk inda kake dan neman tsari

da kariya daga  wajan Ubangiji, ka kiyaye da abinda na

sanar da kai."

Zuhairu ya karbi zobe ya saka a hannunsa sannan

ya yiwa kakansa dattijo Marwan godiya ya tashi ya fita

Washe gari da yamma Zuhairu ya sake yin shiri ya

kama dokinsa ya hau, ya nufi hanyar wannan lambu da

Gimbiya Hasima take zuwa akowane yammaci dan ya

ganta.

Ya ci gaba da tafiya cikin sassarfa da hanzari har ya

Soma hango bakin lambun da Gimbiya hasima take

zuwa. Kafin ya karasa bakin lambun sai ya hangi wasu

barada su kimanin arba'in sanye da kayan fada da

makamai, sun zagaye wasu yammata sun kamasu sun

dora akan dawakansu zasu tafi da su, yammatan suna

kuka da kururuwar neman taimako amma babu wani

wanda zai iya taimaka musu a wajen.

Zuhairu ya saki linzamin dokinsa ya kara azama dan

ya isa garesu yaga abinda yake faruwa da isarsa wajan

sai yaga gimbiya Hasima ce tare da kuyangunta baradan

nan suka kama zasu tafi da su.

Zuhairu ya fusata da ganin wannan aikin zalinci ya

dakawa baradan tsawa ya ce da su "Kai fajirai

kaskantattu ma'abota zalunci da rashin imani, me kuke

nufin aikatawa ga wadannan bayin Allah da ku ka

"Kai

kama."

Baradan nan suka juyo suka dubi Zuhairu, da suka

ga shi kadaine tsaye akan dokinsa sai suka bushe da

dariya irinta mugunta da zalunci, sannan daya daga

cikinsu ya bashi amsa da cewa " Babu shakka ajaline ya

Kusanto da kai wannan waje, har kake tambayar abinda muke nufin aikatawa ga wadannan yammata, bari mu

sanar da kai dan ya zama guzirinka na tafiya barzahu,

zamu tafi da su ya zuwa ga shuwagabannin mu dan,su

zama bayinmu

bukatarmu dasu duk sanda mu kaga dama idan mungaji

dasu ko kuma ansamu kata daga cikinsu tasamu ciki, sai

mu sare kanta dan shayar da jininta ga ababan bautarmu,

wannan shine makomarsu da abinda zamu aikata garesu

masu yi mana hidima da biyan

Idan mun tafi dasu."


Zanci gaba idan kuna biye dani.


Sannan duk mai bukatar sauraron audio din zai iya samu inya fada mana ta comments

 

Comments