Min menu

Pages

Badan da Buhari ba da babu mai iya bacci a Nijeriya inji wani minister

Babu mai iya bacci a Nijeriya da badan Buhari ba inji wani ministerWani ministan Buhari yace badan da Buhari ba da mutane bazasu iya koda barci ba a Najeriya koda kuwa gwamnoni ne.


Ministan Niger Delta Godswill Akpabio yayi magana dangane da gwamnoni masu sukar gwamnatin Buhari da cewa badan da Buhari ba mutane Baza su iya barci ba a Nigeria koda kuwa mutum gwamnoni ne.


Akpabio yace tunda akwai yan sanda, sss da duk sauran jami'an tsaro mutane basa bukatar wani abu a bangaren tsaro. Akpabio ya kara da cewa shugaban kasa wanda zaisa a baku kariya da dare ne Ku shiga gidajenku kuyi barci har gari ya wayene zaku rika cewa ya yaudareku.

 

A wani yanayi mai kama da kulewa Furucin Akpabio na nuni da kalubalantar gwamnonin Dake yankin Niger Delta. 


Yayi wannan furuci ne ranar Alhamis a wajen taron bude ofishin dindin na hukumar cigaban yankin Niger Delta Wanda aka gina a fatakwal,jihar rivers.

Ginin ofishin Wanda aka budeshi a karkashin gwamnatin shugaba Buhari yana hawa na 13 dake ginin storey.

Comments