Min menu

Pages

Babu Mai Daukar Abduljabbar Malami sai Jahili


 TABARGAZA  DA WUCE GONA DA IRIN NA  ABDULJABBAR KABARA


(1) Abduljabbar kabara ya ce wai a cikin Bukhari Sayyaduna Umar R.T.A. ya shaqe wuyan Annabi S.A.W. ya ci kwalar rigarsa wa'iyyazu billah


(2) Ya ce wai a cikin Bukhari annasabtawa Annabi S .A.W. Ya yi wa matarsa Nana Safiyyah R.A.fyade wa'iyyazu billah


(3) Ya ce a cikin Bukhari wai Annabi S.A.W. ya na tura mahaifiyar Anas R.T.A.ta na duba masa tsiraicin matan Madina wa'iyyazu billah


(4) Ya ce a cikin Muslim annasabtawa Annabi S.A.W. shan giya Subhanallah


(5) Ya ce a cikin Bukhari wai katti suna yi wa Ummuna Ai'sha R.A. Layi wa'iyyazu billah


(6) Ya ce wai a auren ummunah Khadijah R.A. da Annabi S.A.W.wai Annabi S.A.W. da iyayensa sun sha giya sun bugu kuma a disi ya gani


(7) Ya ce wai a cikin Bukhari an mayar da Annabi kamar bunsuru sa bo da son mata ya na sabtawa masa Luwadi wa'iyyazu billah


(8) ya ci mutuncin Sayyaduna umar har yana yi masa gori bai taba kashe kafuri a gurin yaqi ba


(9) Haka ya ci mutuncin sahabbai R.T.A. irin su Sayyaduna Usman da Abuhuraira da mugirata bin shuuba da Mu'awiyya da amru bin as da suran su haka ya ce Sayyaduna Anas R.T.A da shi da wasu sahabbai duk ba sahabbai bane makaryata ne


(10) Ya ci mutuncin Manyan Malamai irin su ibn Hazim da ibn taimiya ya ce wa ibn Hajjar munafuki da ace yana duniya sai ya je ya qure shi haka ya zazzgi Muhammad bin Abdulwahab da Albani da bin Baz R.T.


(11) Haka ya keta alfarmar zumunta ya zagi 'Yan uwansa ya zagi ragowar Malaman da suke raye da wadan da suka mutu ya koyawa yaransa zagin duk wani mai mutunci amma bai koya musu addini ba ya barsu da jahilci


Irin wadan nan muguwar aqeedar ta Abduljabbar kabara da yaransa da duk wani mai irin aqeedarsa babu mu babu su in masu shiryuwa ne Allah ya shirye su in kuma ba masu shiryuwa bane Allah ya yi mana maganinsu ya kawo mana karshen su.


 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments