Min menu

Pages

Awa 72 Muka baka ka kwashe duk wasu yarabawa dake jahohin arewa gargadin matasan arewa ga Sunday Igboho

 Mun baka awa saba'in da biyu kayi gaggawar dauke duk wasu yarabawa daga jahohin arewa gargadin matasan arewa kenan ga Sunday Igboho.Hadaddiyar kungiyar matasan arewa dake karkashin Arewa Youth Assembly sun bada kwana uku kacal ga Sunday Igboho akan ya debi duk wasu yarabawa subar jahohin.


Hakan ya faru ne biyo bayan maganganun da yake ta famar yi na cewa ya kafa kasar yarabawa.


In baku manta ba tun ranar laraba Sunday Igboho ya fito yana cewa ya kafa yankinsu na yarabawa kadai.


Wannan dalilin ne yasa matasan arewa suka bashi damar ya debe duk wasu yarabawa kamar yadda ya bukata.

Comments