Min menu

Pages

An ‘Yanto Dalibai 180 A Kaduna -Gwamnati


 An ‘Yanto Dalibai 180 A Kaduna -Gwamnati


Ya zuwa yanzu an ceto dalibai 180 a yayin da har yanzu ba a ga da dama ba tun bayan harin da ‘yan bindiga suka kai makarantar Kwalejin koyar da aikin gona da gandun daji ta gwamnatin tarayya ‘Federal College of Forestry Mechanization,’ dake Afaka a karamar hukumar Igabi.


Rundunar sojin Nijeriya da safiyar yau Juma’a 12 ga watan Maris din 2021 ne suka ‘yanto dalibai 180 wanda mafi yawansu daliban makarantar Kwalejin ‘Federal College of Forestry Mechanization’. 


‘Yan bindigar sun sace dimbin daliban makarantar ne da daren ranar Alhamis da misalin karfe 11 da minti 30, inda suka sace dalibai da wasu ma’aikatan makarantar bayan sun yi harbe-harbe. 


Kwamishinan lura da tsaron ciki gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, a sanarwar da ya fitar a yau, ya ce ‘yan bindigar sun shiga makarantar ne ta Katanga bayan sun fasa katangar. Inda suka yi tafiyar kusan mita 600 kafin su afkawa makarantar. 


Ya ci gaba da cewa ma’aikatarshi ta samu labarin, inda suka sanar da sojin Barikin 1 Division da kuma sashen horaswa ta sojojin sama dake Kaduna. Inda nan take sojin suka kutsa cikin makarantar harma aka yi musayar ruwa a tsakanin sojin da ‘yan bindigar. 


Ya tabbatar da cewa sojin sun ‘yanto mutum 180, wanda ya hada da mata 42, ma’aikata 8 da kuma maza 130. Sai dai ya ce akalla dalibai 30 wanda ya hada maza da mata har yanzu ba a kwato su ba. Wadanda kuma aka kwato su ana duba lafiyarsu musamman wadanda suka samu raunuka. 


Tuni gamayyar jami’an soji, sojin sama, ‘yan sanda da  DSS suka bazama neman sauran daliban, inji sanarwar.

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments