Min menu

Pages

AMFANIN MISKI GA DAN ADAM, DA BA KOWA YA SANI BA

 Muhimmancin Turaren Miski Ga Dan Adam


Shi dai Miski turarene mai kamshi, kamshin kuma mai sa nishadi da annashuwa.


Yana da kyau kwarai da gaske a ce a matsayinki na mace ko da yaushe ya kasance kina da miski a dakinki domin ana so ko yaushe ki rika amfani da shi.Mun riga mun sani shi kamshi abu ne da ya ke kara dankon soyayya, kuma yake dawwamar da ita, sannan miski yana dauke da sinadarai da dama da suke ba wa farjin mace kariya daga cututtuka, saboda haka ana so kullum mace ta rika amfani da shi.


Kalolinshi guda uku uku ne.


Akwai fari mai kamar madara mai kauri: Shi wannan ba’a sashi a cikin farji, saboda a daskare yake bai fiya narkewa ba, sai dai a shafa shi daga wajen farji.Akwai fari kal kamar ruwa, kamshinsa kusan daya ne da mai kaurin, sai dai shi ba shida kauri, to shi za’a iya sawa a matsi da shi.


 Tabbas yana taimakawa har a bangaren auratayya, kuma duk sanda mijinki ya ji wannan kamshin ko bakwa tare ta zai tunaki Zai yi sauri sauri ya dawo gida kinga miski yayi amfani kenan.Akwai jan miski wannan masu fama da matsalan aljanu suke shafashi, domin yana fatattakar aljanu da iznin Allah. Abinda na sani dai idan mai aljanu tana shafa shi in dai an riga an yi mata rukiyya, to suna rabuwa da ita. Amma idan ba ayi ba to za ka ga bata san kamshinsa, ba za ta yi amfani da shi ba.Shi ana shafa shi ne a duk jiki da gabar da ta fi yi wa mai fama da aljanun ciwo. Kun san fa miski asali ya samo yana da kyau kiyi taka-tsantsan wurin amfani da shi, domin ba wai kawai dangwala za ki yi da yatsarki ki saka ba a’a, Za ki nemi ruwan dumi ne ba mai zafi sosai ba, ki je ki kama ruwa da shi, ki wanke wurin sosai, sannan ki samu hankici mai kyau ki goge ko da Tishu. Daga nan sai ki samu “Cotton bud” wato abin sosa kunne.Sai ki dangwalo da shi, sannan ki tura shi a gabanki, ki dan matse kafarki sai ki cire ki jefar. To in sha Allahu ko ‘fant’ dinki kika cire kamshi za ki ji ba Zai yi wari ba. Babu kunya cikin neman ilmi musamman ilmin addini, babban abun kunya a ce mijinki zai kusance ki kuma ya ji farjinki yana wari, haba! wannan ai ba aji.Zaki iya dafa ganyen magarya in ya huce ki zuba miskin kina kama ruwa da shi. Sannan ana so duk sanda za ki saka ‘pant’ dinki to ki diga miskin a kai duk wasu kwayoyin cuta za su mutu da yardar Allah. Ana kuma shafa miski a jiki ana kuma hada shi a cikin Humra yana kuma taimakawa macen da ta haihu kwarai da gaske. Yana da kyau a ce a matsayinki na mace kar a rasaki da wadanna abubuwan Miski:


Ganyen Magarya

Hulba

Habbatussauda

Man Zaitun

Man Tafarnuwa

Khaltufa

Lalle

Zuma

Comments