Min menu

Pages

Abinda ya kamata ku sani akan ginin da yafi kowanne tsawo a duniya


 GININ DAYAFI KOWANE GINI TSAWO A DUNIYA A SHEKARAR 2021


Girman kimiyya da fasaha a duniya kullum fadada suke tare da bada filin kirkiro abubuwan ban mamaki masu girman gaske dake tafiya da zamani kamar fasahar yin keke mai kafa biyu, Babur shima mai kafa biyu, mota, jirgin sama dana kasa, wayar hannu, na'ura mai kwalkwaluwa dai dai sauransu.

A yayin da wani zaiyi Al'ajabin yadda aka gina gada wani kuma mamakin yadda akayi jirgin ruwa zaiyi, Eh!! to hankan zai iya zama da al'ajabi ko akasin haka idan mukayi duba da ginin daya fi kowane gini tsawo a duniya.

Gini mai tsawo shine ginin da zaka sameshi da hawa-hawa (bene) marasa adadi a kalla gini dai mai tsawon Mita 350.

Kamar yadda tarihi ya nuna ginin da dan Adam ya farayi mai tsawo a duniya shine Ginin Babbar dalar Giza dake kasar Misra (Egypt), wannan gini akalla yakai shekara 3,800. Wannan gini shine mafi tsawo har saida akayi ginin Babbar cocin Lincoln a shekarar 1311. Sai bayan kuma an gina Babbar cocin Strasbourg ne dake Faransa a shekarar 1439 ta zama ginin dayafi kowane gini tsawo a duniya har zuwa shekarar 1874.

Bayan wadannan dogayen gine-gine ginin daya zama jagaba shine dogon gini na farko da akayi a Chicago mai tsawon kafa 138ft  Wanda yayi daidai da 42.1m Mai suna gini Gidan inshora (Home of insurance building) a shekarar 1885. Daga wannan lokaci America taci gaba da rike wannan matsayi na Wanda ginin ta yafi kowanne tsayi a duniya har zuwa karshen karni na 20 (20th century) ba'a sami wanda ya wuce shi a tsawo ba har sai a shekarar 1998 bayan an kammala ginin husumiyar Petronas. Daga wannan lokaci kuma aka sake samun wasu yan tagwayen dogayen gini a shekarar 2004 mai sunan ginin Taipei 101 da suka sake samin wannan matsayi har zuwa 2010.

A shekarar 2010 aka kammala ginin da haryau babu kamarsa tsawo a duniya, Ginin BURJI KHALIFA shine gini mafi tsawo a duniya, wannan gini yana Dubai ne, ginin nada tsawon  Mita 828m (kafa 2,717).

Tun a farkon karni na 21 (21 Century), Gabashin tsakiyar kasar China da yankin kudu maso gabashin Asiya suka karfafa tsarin fasahar yin dogayen gine-gine.

Comments