Min menu

Pages

An sake samun matar aure ta kashe mijinta har lahira bisa wani karamin dalili.

 Ta kashe mijinta har lahira saboda wannan dalilin kawaiAn  sami Wani labari mai matukar rikitarwa daya dauki kwanaki yana zagaya a kafafan yada zumunta na wata matar aure mai shekara 22 dake dauke da tsohon ciki data kashe mijinta mus har lahira.

Matar mai suna Faith Okiemute  a ranar litinin 15 ga watan maris 2021 ta kashe mijinta mai suna Edafe Unuakpor, mazaunin Ekrejebor a karamar hukumar Ughelli dake jihar Delta.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta kashe mijin nata bayan tayi zargin yana kula wasu matan a waje.

Bayanai sun bayyana Faith Okiemute tayi amfani da katuwar wuka wajen kisan, Da farko saida ta sare masa hannu daga bisani kuma ta gabza masa Wani saran a tumbi wanda a take yace ga garinku.

Ma'auratan sun shafe a kalla shekara biyu kuma suna da 'ya karama a tsakanin su.

Faith Okiemute tana da yara biyu da mijin data aura na farko.

A shekarar 2019 Zuwa 2020 dai a Najeriya an sami matsaloli da dama masu alaka da wannan a tsakanin ma'aurata.

Comments