Min menu

Pages

Ƴan Najeriya za su soma biyan harajin sayen katin waya ta banki

Ƴan Najeriya za su soma biyan harajin sayen katin waya ta banki


Babban bankin Najeriya ya bijiro da sabon tsarin haraji kan kwastamomin da ke sayen katin waya ko 'data' ta asusun ajiyar bankinsu.


Bankin ya ce daga wannan Talatar, za ake cire harajin N6.98 kan kowanne kati ko 'data' da aka saye na layin waya.


Ya ce sabon tsarin na cikin yarjejeniyar da aka cimma da bankuna da kamfanonin sadarwa bayan wata tattaunawa a jiya Litinin kan bashin naira biliyan 42 da ake bin kamfanonin sadarwa.


Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa haɗin-gwiwa da aka fitar tsakanin babban bankin da kamfanonin sadarwar.


Wannan tsari dai zai soma aiki ne daga wannan Talatar wato 16 ga watan Maris din 2021.


 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments