Min menu

Pages

Abubuwa guda goma da duk wata mace ke bukatar ji daga gurin na miji

Abubuwa da duk wasu mata ke bukatar ji daga gurin samari Akwai abubuwa da duk wata budurwa ke bukatar ji daga gurin na miji saurayi wanda idan saurayi yana fada mata za taji a duniya tafi so da kaunarsa.


Su mata wasu mutane ne da kalamai kanyi tasiri matuka a zukatansu hakan yasa suke son duk wani saurayi daya kware a kalamai.


Saidai cikin kalaman ma za kuga wasu sunfi wasu jan hankali da birgewa tare da kama zuciyar budurwa.

Dan haka muka zo muku da wasu daga ciki guda goma wanda suke da tasiri sosai.


Ina sonki har cikin bangon zuciyata


Kinada kyau wanda ya kere sauran mata dan haka har kunya nake nayi photo dake karna bata miki photon saidai kyawunki nima karamin kyau yake.


Kullum ina dada godiya ga Allah dana sameki a matsayin masoyiya.


Zan iya karasar da rayuwata dake.


Ke kadai ce ke korar damuwa a fuskata.


Wasu abubuwa da duk wata mace take so ga saurayi


Ke ta daban ce domin duk abinda kike birgeni yake.


Kin canja ni zuwa mutum na kwarai


Koda yaushe kina yimin abinda yake sani farin ciki.


Rayuwata ta cika tsaf tunda na same ki.


Wadannan kalaman suna matukar tasiri a zuciyar mata don haka duk mai soyayya ya gwada amfani dasu yaga zai bani labari.

Comments