Min menu

Pages

 Yanzu muke samun rahoto daga wata majiya mai tushe cewar an budewa yan shi'a wuta.
Lamarin ya faru ne yau a Abuja inda jami'an tsaro suka budewa almajiran malam zazzaki wuta.


Wanda har aka samu daya daga cikin yan shi'ar ya rasa ransa kuma aka raunata wasu da dama.


Bayan haka kuma jami'an tsaron sun sake yin awun gaba da wasu daga cikin yan shi'ar.


Da farko kafin faruwar abin anga yan shi'ar sun fara fitowa maza da mata rike da alluna mai dauke da tambarin shugaban nasu zazzaki kafin daga baya yan sanda su tsayar dasu to amma sai suka ki tsayawa.


To da yan sandan suka ga haka sai suka harba musu barkonon tsohuwa, daga nan kuma sai aka fara jin karar bindinga inji shaidun da suka gani da ido.


Comments