Min menu

Pages

Yan boko haram sunki sakin leah sheribu ne kawai domin su hada musulmai da kiristan kasar nan gaba

 Yan boko haram sunki sakin leah sheribu ne kawai domin su hada musulmai da kiristan kasar nan gabaMai magana da yawun shugaban kasa lai Muhammad ya bayyana cewar yan boko haram din sunki sakin leah sheribu ne kawai domin su raba kan yan kasar kirista da musulmi koma don su hadasu fada da gaba a tsakani.

Leah sheribu dai ita ce dalibar da yan boko haram suka rike tsawon shekaru tun lokacinda suka dauke daliban makarantar dapchi.

Wanda duk daliban da aka dauke ta tare dasu an sako su ita kadai ce ta rage yan boko haram din basu sake ta ba.


Wannan abin ya jawo maganganu masu tarin yawa a kasa musamman tsakanin kiristoti da musulmi.


Wanda hakan yasa kiristotin kasar ke kalubalantar musulmi harma wani lokacin suke kwatanta su da yan ta'adda.

To saidai gwamnatin tarayya tace rike dalibar da akai kawai so ake a tada husuma tsakanin musulmi da kiristan kasar wannan kawai shine shirin yan boko haram din.

Daga karshe gwamnatin tarayya ta sanar da cewa yan kasar su hada kansu kar wasu daga gefe

Comments