Min menu

Pages

Yan bindinga sun kone Rumbuna da gidaje tare da kashe mutane masu yawa a jihar Katsina

 Mutane dauke da makami da ake zaton yan bindinga ne sun kashe mutane ashirin tare da kone rumbuna da gidajen mutane a wasu kauyukan KatsinaYan Bindiga Sun Kashe Mutane ashirin Da Kone Gidaje Da Rumbuna A Kauyukan Jihar Katsina


Yan bindigar sun kone gidaje sama da dari biyu da runbunan hatsi da dama sannan sun kashe mutane ashirin


Ranar talata da yamma ne, 'yan bindiga dauke da muggan bindigogi suka kai harin a kauyukan fan dogari da kuma maradi da da Damawa da Cikawa da Suda da Gayuna da ke gundumar Wurma a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, inda suka kashe sama da mutane ashirin must har lahira tare da kona gidaje da dama a garuruwan 


Yan bindingar sun shigo wadannan kauyukan ne akan babura suka fara harbin mutane babu ji babu gani.

Don gaskiya mutanen da suka kashe sun fi ashirin,saboda kauyuka biyar ne suka shiga, akwai inda suka iske ana biki, suka yi ta harbin mutane, kuma ko da mutum ya ruga sai su bi shi su harbe shi. 


Sun bankawa rumbunar ajiyar kayan abinci da dama, sun kone su kurmus har da gidaje sama da dari biyu. 

Mutanen wadannan garuruwa duk sun tsere an kone garuruwan ba wanda ba'a sa wuta ba.


Majiyar ta  kara da cewa 'yan suntiri na garin Wurma da makwabta hadin gwiwa da jami'an tsaro sun bi su har dajin Safana, amma an ce ba'a gansu ba. 


Har sadda muke maganar nan da nike da kai ba'a gama tantance yawan barnar da suka yi ba na asarar rayuka da dukiyoyi.


Allah ya kare mana kasarmu

Comments