Min menu

Pages

Yan bindinga sun kira Shugaban kasa daya shiga jeji su tattauna dasu idan yana son zaman lafiya a kasar

 Yan bindinga sun kira Shugaban kasar Nigeria da yazo su tattauna idan har son zaman lafiya yake a kasaLabarin da muke samu yan bindinga sunyi ikirarin idan har zaman lafiya shugaban kasar yake nema to yai sauri yaje su tattauna dashi.


Sun nuna zuwan shugaban kasar domin sulhu garesu itace hanya guda da zai nuna yana son zaman lafiya.


Yan bindingar dai wasu hadakar mutane ne da suke kashe mutane ko kuma su dauke sai an biya kudin fansa wanda abinda suke ba karamin ciwa al'ummar kasar tuwo a kwarya yake ba.


Domin babu ranar da zata zo ta fadi ba a samu labarin yan bindingar sun shiga gari tare da kashe mutane ko kone musu gida ko kuma rumbuna ba.


Domin ko rannan yan bindingar sun dauke wasu dalibai yan makaranta wanda aka samu suka sako su.


Akwai gwamnoni da suke zaman sulhu da yan bindingar domin ganin an kawo karshen matsalar amma har yanzu shiru.

To sai yanzu ake samun sanarwa daga yan bindingar suna cewa Shugaban kasar yaje yai zama dasu idan har yana so ya samu zaman lafiya a kasar sa ta Nijeriya.


Suka kara da cewa ai zai iya shiga jeji shima domin lokacin da yake yakin neman yaci zabe babu inda baya shiga dan haka ya shigo jeji domin ya zauna dasu.


Comments