Min menu

Pages

Da dumi-duminsa wasu fusatattun matasa sun kashe hausawa tare da kone musu kayayyaki a Jihar Edo

 Da dumi-duminsa wasu fusatattun matasa sun kashe hausawa tare da kone musu kayayyaki a Jihar EdoYanzu labari yake zo mana cewar wasu fusatattun matasa sun kunnawa kayan hausawa wuta tare da kone musu kayayyaki sannan sun kakkashe wasu da dama.


Kamar yadda rohoton yazo mana daga ogheghe cikin birnin Benin, wasu fusatattun matasa cike da bakin ciki sun tare wani yanki da hausawa suke zama tare da sawa gidajensu wuta da kayayyakin su sannan suka rufawa wasu mutanen da sara suka kashe da dama.


Wannan ya faru ne bayan taron hausawa sun samu wani dan asalin gurin sun dake shi a cewarsu.


Wanda hakan yasa suka kashe shi domin sunce yana daga cikin mutanen da yake daukar musu baburansu inji hausawan.


Wannan yasa mutanen gurin gaba daya suka rufarwa hausawan tare da kone musu kayayyaki masu yawa.


A yadda mutanen yankin suke cewa idan har zasu kama mutumin yankinsu su daka to suma Basu ga abinda zai hanasu su dauki mummunan mataki akan hausawan ba.

Comments