Min menu

Pages

YADDA AKE HADA TURAREN FESAWA A JIKI A GIDA

 YADDA AKE HADA TURAREN FESAWA A JIKI A GIDA Idan ka kasance ma'abocin yin amfani da turaren fesawa ne to ga dama ta samu ta yadda zaka iya hada irin kalar turaren da kakeso a gida ba tare da ka siyo ba.

Da farko idan kana son hada turare mai kyau, kuma na fesawa hanyar mai sauki ce kuma kayan ba wani yawa garesu ba. 

KAYAN HADI

Madarar turare: zaka samo madarar turare irin Wanda kakeso, amma idan kanason yayi kyau kuma yayi yadda ba Wanda zai gane irin kalar turaren dake jikinka saika hada kala dabam-dabam.

Methanol (ruwan sanyi):methanol ana sayar dashi a kasuwa wajen masu saida kayan cosmetics.

YADDA AKE HADAWAZaka debo madarar turarenka 500ml ka zuba a cikin ruwan methanol liter daya ka girgiza. Bayan ka tabbatar da sun gama haduwa saika zuba a kwalbarka ko robarka ta fesawa ka rika fesawa abinka. 

Abin duba anan shine idan har kaji turarenka baiyi kamshi ba sosai saika kara ruwan madarar turaren har yakai yadda kakeson kaji domin wani madarar turaren bata da karfi kamar wata.

Comments