Min menu

Pages

Ya kashe Matarsa Bayan Sun Dauki Hoton Selfie


 Ya kashe Matarsa Bayan Sun Dauki Hoton Selfie

An kama wani magidanci Hakan Aysal mai shekaru 40 da laifin kashe matarsa mai juna biyu Semra Aysal mai kimanin shekara 32 a duniya yayin gudanar da hutun shakatawar su a tsaunin da ake kira 'Butterfly Valley' a birnin Mugla da ke kasar Turkiyya.


Mijin nata dai ya ingiza matar tasa mai dauke da cikin wata bakwai daga kan tsaunin da ke da tsawon kafa 1,000, inda nan take ta ce ga garinku nan.


Ma'auratan dai suna daukar hoton Selfie ne akan tsaunin, bayan sun gama sai mijin nata ya tura ta ta fado.

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments