Min menu

Pages

Sanarwa mai mahimmanci ga masu son mallakar wayar iphone

 Sanarwa mai mahimmanci ga masu son mallakar wayar iphone 


Duba yadda zaka gane jabun Iphone ( fake iphone)Kayan kamfanin apple kusan shine kaya mafi kyau da bada sha'awa a yan wadannan shekarun, mutane kanyin rige rige wajen sayan wayarsu ta Iphone wadda ta fito kuma ake matukar yayinta domin duk wani hadadden saurayi ko hadaddiyar budurwa za kaga ita ce a hannunsa.


Harma wasu na ganin in baka rike da irin wannan wayar to kai ba babban yaro bane ko kuma ba ke ba babbar yarinya bace.

Wannan yasa wasu kan kirkiri wata waya wanda take kama da Iphone din suna sayarwa mutane a matsayin original iphone ce.

Mun samu irin wadannan korafe korafen a gun mutane masu yawa wadanda suka sai irin wadannan jabun Iphone din ( fake iphone) wannan shine yaja hankali na naga ya dace na nusar wa mutane hankali akan hanyoyin da za subi su gane iphone ta gaskiya da kuma jabu (fake) domin gudun kada suje saya a caka musu maras kyau a matsayin mai kyau.

Ga hanyoyin da za kubi ku bambance iphone ta asali da kuma jebu (fake)

√ screw ( Noti) Akwai wasu abubuwa masu kamar notina da zaku gansu jikin wannan foton dake kasa, zaku gansu su biyu a kusan gurin cajin wayar (charging point) daya ta bangaren dama daya kuma ta hagun, to ku duba sosai za kuga suna madaurin photon tauraruwa ne a jiki star 🌟  ba kamar dayan bane mai foton cross (+) to idan kuka ga sunada wani ba irin wannan ba to gaskiya akwai matsala.√ Madannai guda biyu da ake ganinsu ( physical button) abinda ya kamata ku fara dubawa idan zaku sayi waya iphone shine ku lura sosai da madanna guda biyu dake bangaren hagu da dama, idan ka duba kaga makunnar tana daidai tsakiya ta bangaren dama,yayinda volume dinta yake bangaren hagu a tsakiya ta sama to wannan ma iphone ce ta asali sannan idan kaga sabanin haka to kada ku saya.√ fuskar iphone din ( screen) shi screen din iphone ta gaskiya zaku ga screen dinta yanada matukar kyau da dauke hankali ba kamar na sa jabun (fake) ba wanda shi bashi da wani kyau da daukar hankali.√ Tambarin apple a bayan kowacce iphone akwai tambarin apple (logo) domin suma sauran masu yin jabun Iphone din (fake iphone) suma sun saka wannan logo din, abinda za kuyi ku gane iphone ta gaskiya cikinsu shine kusa dan yatsan hannunku akan logo din kimtsatstse ne wanda kamar sakawa akai to karku dauki wannan wayar jabu ce.√  welcome screen duk wanda zai sayi iphone to ya kunnata, wacce bata da kyau ko kuma bata asali bace idan an kunna zata nuno wani abu mai kama da welcome sabanin original iphone din da ita iya photon iphone dinne yake bayyana idan an kunnata.√ app store shima wani guri ne a jikin wayoyin iphone, idan ka kunna ta cikin home screen zakaga tambarin app store din saika danna shi idan kaga ya dan bata lokaci wajen load ko kuma ya kaika wani waje kai tsaye to wannan itace cikakkiya.

√ Gurin Sim card indai iphone ta gaskiya ce to gurin sa Sim card dinta guda daya ne duk wata iphone da zaka saya in kaga wani guri dake nuna karin gurin sim card ne to gaskiya karka saya domin fake ce.


√ Camera duk wata iphone indai ta gaskiya ce za kuga camerar ta tanada matukar kyau da daukar hankali ba kamar sauran wayoyi ba to dan haka idan za ku sayi iphone ku duba camera dinta idan har kuka ga bata da kyau to fake ce.Comments