Min menu

Pages

Ya kamata a soke lefe amma mazan sune za suna daukar yin dawainiyar komai inji Mal Bin Uthman

 Ya kamata a soke lefe amma mazan sune za suna daukar yin dawainiyar komai inji Mal Bin UthmanShehin Malami nan Bin Uthman yace yanzu lokaci yayi daya kamata a soke lefe gaba daya a kasar hausa idan har an tashi yin aure.

Ya baiyana haka ne ranar juma kafin ya fara gabatar da tafsiri a masallacin dake kundila jihar kano.

Yace idan aka tashi aure sai kuga ana ta kawo abubuwa iri iri, har ya jero sunan lefe a ciki kuma shima yace ya kamata a soke shi.

Lokacinda malamin ya fadi haka mutane da yawa sun nuna jin dadinsu harma sukai ta amsawa da cewar hakan ya dace.

Malamin saida yai tambayar cewa yana so a fada masa waye yace ayi lefe sai aka ce babu kawai dai al'ada ce irinta kasar hausa.

To saidai ta wani gurin malamin ya nuna cewa kamata yayi idan zaka auri mace kamata yayi ka sayawa gidanka komai saidai tazo ta tarar a gidanka.

Batun kayan lefe dai an jima ana tattaunawa a kai to saidai maza sunaga koda an soke lefe saidai mace tazo da kayan saninta.

Comments