Min menu

Pages

Wata daliba ta yaga rigar malaminta saboda ya hanata rubuta jarabawa

 Wata daliba ta yaga rigar malaminta saboda ya hanata rubuta jarabawaDa safiyar yau ne wata daliba dake karatu a wata makaranta ta yaga rigar malaminta a dakin jarabawa saboda ya hanata rubuta jarabawa.


Lamarin ya faru ne bayan malamin ya kamata da kayan da ba'a amince dalibai su shiga dakin jarabawa dasu ba saboda satar amsa.


Sannan ya bata form ta cike a matsayin wacce aka kama da satar amsa,wannan abin bai yiwa budurwar dadi ba dan haka bayan an gama jarabawa sai ta tare malamin tana fada masa maganganu harma ta kama rigarsa.


Sauran mutane yan uwan dalibar sunyi kokarin shiga tsakanin dalibar da malamin amma duk da haka saida ta yaga masa Riga.

Kalli bidiyon anan

Comments