Min menu

Pages

DA WAHALA A KAWO ƘARSHEN TA'ADDANCI A NAJERIYA

DA WAHALA A KAWO ƘARSHEN TA'ADDANCI A NAJERIYA


Mutanen arewa akwai su da matsala mai girma wanda suna bada gudummawar ƙarfafa ƴan ta'adda, amma suna zargin wanda yake ƙoƙarin kawo karshen ta'addanci a wannan ƙasar sau da dãma idan ka kasance kana shiga tsakanin gwamnati da ƴan ta'adda domin kawo karshen tashin hankali toh Yan Najeriya da ake kashewa sune zasu fara zargin ka da ta'addanci ko haɗa baki da ƴan ta'adda.


Har kullum ina ganin irin abubuwa da suke faruwa a yanar gizo akan dukkan waɗanda suke ƙoƙarin tona asirin ƴan ta'adda wajan yi musu kazafi da zargi mara kan gado, Datti Assalafiy mutane jahilai dayawa sunyi zargin sa wai a ina yake samun irin waɗannan labaran ai shima boko haram ne don Allah kaji irin zancen mutanen mu na arewa basa fatan alkhairi zuciyar su ta cika da hassada.


Farkon wanda zasu fara maka zagin ƙasa a wanann kasar sune ƴan arewa wanda a dalilin kawo musu zaman lafiya ka bada rayuwar ka amma suna kokarin ganin bayan ka, haka shekarun baya na fara tona asirin wasu ƴan ta'adda amma wallahi zargi yasa dole na daina ban tsira ba a wajan jami'an tsaro haka ban tsira ba a wajan mutanen gari, shiyasa na daina yawan rubuce-rubuce domin nan muka ƙware wajan bincike yanzu mun bari, anya kuwa zaku iya kawo karshen wannan matsalar a wannan ƙasar.


Yanzu Dr. Ahmad Gumi me yake buƙata a wajan mu banda addu'a da fatan alkhairi, amma kullum bamuda aiki sai zargi da hassada da mugunta haba jama'a wallahi mu shiga taitayimu.


Allah ya shirye mu mu gane Allah ya kawo mana ƙarshen ta'addanci a wanann kasar.

 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments