Min menu

Pages

Tace mijinta ya kasa yi mata ciki dan haka a raba auren inji matar aure ga alkali

 Tace mijinta ya kasa yi mata ciki dan haka a raba auren inji matar aure ga alkaliWata matar aure ta maka mijinta a kotu gaban alkali sannan ta nemi mai shari'a daya raba aurensu tsakaninta da mijinta tunda dai ya kasa yi mata ciki.


Matar kuma tace ita a shirye take data mayarwa da mijin nata kudin sadakin daya bata naira dubu ashirin duk kuwa da cewa auren nasu yakai shekaru goma.


Matar dai sunanta murwanatu muhammad kuma sunan mijin nata Iliyasu da suke auren a garin Kaduna.


Matar ta nuna sun jima suna tare da mijin nata domin a kalla za sukai shekaru goma amma har yanzu ya kasa yi mata ciki dan haka take neman kotu ta raba auren nasu shida ita.


Mijin yace koda zasu rabu to ya kamata matar ta dawo masa da kudinsa da yace yana binta bashi har dubu goma sha bakwai.


Miji da matar sun jima da aure saidai har yanzu basu samu karuwa ba shine matar ke zargin mijin nata da baya haihuwa dan haka tace ita dai saidai a raba auren.


To saidai alkalin ya umarce su cewar suje asibiti domin ayi musu gwaji.

Comments