Min menu

Pages

Gwamnatin Kano ta sayo sabbin motocin daukar mutane sakamakon yajin aikin da yan adaidaita suka shiga.

 Gwamnatin Kano ta sayo sabbin motocin daukar mutane sakamakon yajin aikin da yan adaidaita suka shiga.



A yau dinnan har gwamnatin Kano tayo odar wasu motoci domin daukar mutane zuwa ko ina a cikin kwaryar kano.


Tunanin da mutane suke sayo wadannan motocin baya rasa nasaba da yajin aikin da yan keke napep suka shiga a kano da safiyar yau.


Yan adaidaita sahun sun shiga yajin aikin ne bisa wani haraji da gwamnatin kano din ta saka musu wanda su suke ga baza su iya biyan haka ba, sun nemi ayi musu ragi amma ba'a cimma matsaya ba hakan shine yasa suka fada yajin aikin na sai baba ta gani.


Ko yau mutane sun sha fama a tafiye tafiye a kano domin babu abin hawa wanda hakan yasa mutane da yawa sai takawa sukai da kafafunsu yayinda yan makaranta da dama sai hakura sukai da zuwa makarantar saboda nisa kuma baza su iya tafiya a kasa ba.


To saidai an hangi wasu dogun motocin wanda aka kawo su kuma ana tunanin gwamnatin kano dince ta iyo odar su domin su maye gurbin adaidaita din da suka shiga yajin aikin.

Comments