Min menu

Pages

Shugaban sojojin kasa ya sanar da shirinsu na daukar sojojin haya na kasar kamaru da chadi a shirinsa na yaki da yan boko haram.

 Shugaban sojojin kasa ya sanar da shirinsu na daukar sojojin haya na kasar kamaru da chadi a shirinsa na yaki da yan boko haram.Shugaban hafsan sojojin kasan Ibrahim attahiru ya fadi hakan ne duk a Shirin da suke na yakar yan ta'addan boko haram din da suka fitini wasu yankunan a Nijeriya.

Shugaban sojojin yace babbar manufarsa itace yaga an kawar da wannan ta'addancin da ake a kasar kuma yana sa rai hakan zai iyu da karfin ikon Allah, ya kara da cewa shi yanzu bashi da wani buri face yaga kasa ta zauna lafiya hankulan mutane ya kwanta.

Sannan zamu kara jajircewar game da nasarar da rundunonin da suke yaki da yan ta'addan domin ganin an kawo karshen matsalar cikin kankanin lokacin sannan zamu hada karfi da karfe ga sojojin kasashen chad da kamaru domin abin yazo da sauki.

Sannan ya kara da cewa zasu karo kayan aiki domin ayi aikin ba tare da fargabar komai ba.

Yan kasa su dage da addu'a domin tanada amfani sosai.

Comments