Min menu

Pages

Shugaban kasar America yayi barazanar sanya takunkumi ga Nijeriya idan basu amince da auren jinsi ba.

 Shugaban kasar America yayi barazanar sanya takunkumi ga Nijeriya idan basu amince da auren jinsi ba.




Sabon Shugaban kasar Joe Biden ya sabunta sha'awar america na kawo yanci da ci gaba ga rayuwar yan luwadi da madigo tare da kuma daidaita rayuwar maza da mata a kasashen da aka ga suna muzgunawa masu irin wannan harkar. A yayin da yake sabunta yarjejeniyar da aka kulla da wasu kasashe tun a lokacin gwamnatin shugaba obama a shekarar dubu biyu da sha daya 2011, wanda ya nuna sha'awar kare wadannan al'umma.

A sabuwar yarjejeniyar daya fitar a satin da ya gabata ya umarci dukkannin jakadodin kasashe da kuma shugaban nin zartarwa dasu kare hakkin yan madigo da yan luwadi a ko ina suke a fadin Duniya.

Sabuwar kaddamarwar da shugaban kasar yayi ta fito fili baro baro inda ya umarci kungiyoyin samar da bayanai na kasashe da su tashi tsaye su yaki duk wani tsari ko wata doka dake tauye hakkin masu sha'awar auren jinsi.

A dokokin da ya fitar ya bawa kungiyoyin da suke kasashen waje umarni kai tsaye da samar da bayanai akan duk wani take hakki da suka samu na masu auren jinsin.

Nigeria ta fuskar hukuma na daga cikin kasashen da suka soki bawa masu auren jinsi yancin kai tun a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar jonathan, shugaba jonathan ya sanya hannu akan dokar hana auren jinsi tun watan janairu 2014 inda dokar tace Duk wanda aka kama da alaka da auren jinsi zaiyi shekara 10 zuwa 14 a gidan yafi.

Shugaban kasar ta America ya tabbatar da kakkarfar barazana ta sanya takunkumin tattalin arziki tare da hana visa ta shiga America ga duk kasashen da suka bijirewa umarnin. 

Najeriya a matsayin kasa mai cike da bambamce-bambamce ta fuskar al'umma tare da karfin tasirin da addinai ke dasu hakan zai iya jawowa tayi hannun riga da umarnin na Joe Biden, A yayin da kuma take kokarin ganin Kasar ta farfado daga matsalar talauci da ta'addanci wanda take fama dashi. Wannan yazowa Najeriya da barazana ta fuskar diflomasiya. Har yanzu dai ba'a samu Wani martani ba daga Najeriya kan kudurin na Joe Biden.


Comments