Min menu

Pages

Sheikh Gumi yace sojoji ne basu so yaki da yan ta'adda ya kare saboda abinda suke samu

 Sheikh Gumi yace sojoji ne basu so yaki da yan ta'adda ya kare saboda abinda suke samu





Masani kuma fitaccen malamin Musuluncin nan  Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya nuna zargin cewa sojojin Nijeriya na amfana da yaki da kasar ke yi da ta’addanci shi ya sa ba sa so matsalar ta tsaron ta kare a kasar.


Malamin ya yi zargin cewa zunzurutun makudan kudaden da gwamnati ke kashewa a wurin yaki da ta’addanci da yan ta'addan ya sa yawancin manya manyan sojoji ba sa kaunar a kawo karshen matsalar dake addabar kasar.


“Sojoji ba sa taimakawa ko kadan saboda su ke amfana da tabarbarewar sha’anin tsaro,” inji shi a lokacin hirar da yayi da wani gidan talabijin na ARISE TV.


Sheikh Gumi ya bayyana haka ne yayin karin haske game da ziyarar kwanan nan da yake kaiwa dazuka don yin da’awa ga ’yan bindiga domin su rungumi zaman lafiya su daina ta’addanci da tada hankalin kasa.


“A shirye ’yan bindigar suke su ajiye makamansu su koma rayuwarsu yadda suka saba a baya kamar sauran mutane muddin dai Gwamnatin Tarayya za ta biya bukatarsu da bata taka kara ta karya ba, ta gina musu makarantu da sibitoci ta samar musu da ruwan sha.


“Suna yawan kokawa cewa sojoji na kashe mutanen da babu ruwansu basu ji ba kuma basu gani ba. Shi ya sa suka fara daukar makamai. Ko ta ina suke samun makamai? Suka fara yin garkuwa mutane wanda shi ya haifar da wannan aikin soji.


“Amma a shirye suke su ajiye makamansu su koma rayuwa kamar sauran ’yan Najeriya idan za a gina musu makarantu da asibitoci a samar musu da ruwan sha.


“Akwai kuma zargin cewa sojoji ba sa so a kawo karshen rikicin saboda da biliyoyin Nairori da ake ba su don yakar ta’addanci. Saboda haka su ma sojojin ba sa taimakawa.


“Ina yaba wa ’yan sanda da Shugaban ’Yan Sanda musamman saboda ya taimaka mun je mun gana da waddannan mutane; amma su sojoji babu alamar za su taimaka, ba su ba da hadin kai ba; ban san dalili ba.”

Comments