Min menu

Pages

Rikici mai zafi ya barke a jihar Oyo tsakanin yan jihar da yan arewa

 Rikici mai zafi ya barke a jihar Oyo tsakanin yan jihar da yan arewaYan kabilar yarabawa sun kai mummunan farmaki ga yan uwa yan arewa cikin garin ibadan na jihar Oyo.

Abin ya kai ga hasarar rayuka da kayayyaki na yan uwanmu yan arewa

Kiranmu na gaggawa ga gwamnati dama masu ruwa da tsaki da suyi saurin kaiwa dauki gare su domin kubutar dasu daga wannnan abin da yake faruwa.Yan kabilar yarabawa sun dirarwa yan uwa yan arewa a garin ibadan yanzu dake jihar Oyo Abin tun jiya yake faruwa har yanzu wanda hakan ya kawo mummunar hasara wanda bazata kirgu ba.

An samu sahihin labarin daga kungiyar arewa writers inda itama tace ta samu sahihiyar sanarwar ne daga majiya mai karfi inda yarabawan suka kashe yan arewan maza da mata wanda ba'a san yawansu ba.Lokacin da abin yake faruwa mafiya yawan yan uwanmu yan arewa basu samu sun kwana a gida ba saboda ta'addancin da aka kai musu mummuna.

Wannan dalilin yasa kungiyar marubutan arewa a kafofin sadawarwa karkashin jagorancin abba sani suke kira ga gwamnatin Nigeria data gaggawar daukar mataki kuma tai saurin kaiwa dauki ga yan uwa dake zaune acan.

Sannnan aja kunne ga masu aikata wannan abin domin gujewa faruwar tashin hankali.


Comments