Min menu

Pages

Sahabban Annabi yardaddun Allah ne, ga dalilai hamsin

 Sahabban Annabi yardaddun Allah ne, ga wasu dalilaiSahabban manzon Allah ba abin zagi bane domin sun bada mahimmiyar gudunmawa wajen daudaka addinin Allah ga kadan daga darajojinsu.

√ Su suka fara kadaita Allah bayan aiko manzon Allah

√ sune suka fara sallah cikin wannan al'ummar
√ Sune suka fara azumi

√ Sune suka fara fidda zakka.

√ Sune suka fara aikin hajji da umra bayan aiko annabi.

√ Sune suka fara hijira domin Allah

√ Su aka fara kashewa saboda Allah

√ Da dukiyarsu aka sa harsashin gina addinin Allah

√ Su aka fara yiwa azaba saboda addinin Allah

√ Sune abokan Annabi

√ Sunga Annabi ido da ido

√ Sunji Annabi gaba da gaba


√ Sun zauna da annabi guri daya

√ Sunyi tafiya tare da annabi.

√ Sunbi Annabi sallah sauda kafa

√ Sunyi yaki tare da annabi

√ Sunci abinci tare

√ Annabi malaminsu limaminsu.

√ Duk inda aka kira masu imani sune farko

√ Duk inda aka fadi masu hali mai kyau za kaga sune.

√ Allah yana son su
√ Allah yana son masu tuba, suna yawan yinsa.

√ Allah yana son masu tsarki sukwa suna yinsa.

√ Masu dogaro da Allah ne.

√ Allah yana cewa Annabi yayi shawara dasu.

√ Masu dogaro da Allah ne


√ Allah yace da annabi yayi shawara dasu

√ Allah yace da annabi yayi musu afwa.

√ Allah yace da annabi ya nema musu gafara
√ Masu yaki sahu sahu

√ Sune suka fafata a yakin badar har akace babu dan wuta a cikinsu.

√ Mutum 70 daga cikinsu sunyi shahara a Uhud wajen kare addini.

√ farisawa sunsha kashi a hannunsu.

√ Sune suka rushe hancin rumawa masu sakandami a kasa.

√ Sune suka bude iraq

√ Sune suka karbo syria daga hannun runawa da baitul maqdis

√ Sune suka rushe gunkin lata da uzza.
√  Sune suka kawo musulunci Africa kafin yaje ko ina bayan makes.

√ Sune suka fara haddace alqurani mai girma a karon farko kuma suka rubutashi.

√ Sune idan sukayi sadaka mudu daya yafi dutsen Uhud

√ A cikinsu aka samu wanda kafarsa tafi dutsen Uhud nauyi saboda imaninsa.

√Allah ya yarda dasu sun yarda dashi.


√ Allah ya sanya nutsuwa a zukatansu

√ Allah ya shaidi imaninsu

√ Sune suka rawaito mana rayuwar annabi SAW maganganunsa da ayyukansa.

√ Sune suka yada musuluncin harya iske mu.

√ Sune Allah ya rada musu suna masu kaura kuma masu taimako

√ Sune Allah ya shaidesu da gaskiya.

√ Sune wadanda ba ayi ba kuma baza ayi irinsu ba bayan annabawa da manzanni.

√ Duk wanda ya zage su to Allah ya tsine masa

Ba kamata ana zaginsu ba.

Comments