Min menu

Pages

Mutane Biyar da duk mai hankali ya kamata ya kaurace musu

Mutane Biyar da duk mai hankali ya kamata ya kaurace musu



Ka fadamin su waye abokan ka, ni kuma zan fada maka kai waye. Domin kuwa duk irin mutanen dake zagaye dakai suna da mahimmiyar rawar da zasu iya takawa a rayuwarka walau ta hanya mai kyau ko marar kyau dole suna da tasiri. Idan harka zagaye rayuwarka da mutane masu fishi, dacin zuciya da kuma mummunan tunani, rayuwarka zata tabbata cikin damuwa, idan kuma ka zagaye rayuwarka da mutanen kirki rayuwarka zatayi matukar kyau.

Dan uwa ka duba wannan rubutu dakyau bisa lura ta ilimi hakika kowane mutum bazai rasa mutanen da suke cutar da rayuwarsa ba kuma suke da matukar tasiri cikin yau da goben saba,wasu abokai ne,wasu dangi ko yan uwa, to Dan uwa lokaci yayi da zaka kauracewa tsarin irin wadannan mutane masu hadari. Anan zan kawo muku mutane 5 daya zama dole a kaurace musu domin rayuwarka ta duniya da lahira tayi kyau, idan ka sansu ya rage naka kaci gaba da zama dasu ko ka takaita koma ka kaurace musu baki daya.

1. Marar Gaskiya

Gaskiya abace wanda kowane mutum ke bukata ta fuskar kowace alaka. Mutane marasa son gaskiya a kowane lokaci basu da buri face suga cewa duk Wanda ke tare dasu sun zama tamkarsu, idan harya kasance kana tare da irin wadannan mutane tofa kana cikin waki'a babba domin dabi'arsu saita zubar maka da daraja matukar baka rabu dasu ba. Idan har mutum zaiyi maka zancen karya ko rashin gaskiya to baka da daraja ko kadan a wajensa ka kiyaye zama dashi shine kawai yafi don karya alkawari cin amana abi ne mai sauki a gareshi.

- Masoyan Nura m Inuwa sun fara zanga zanga

- Kasa mafi kankanta a Duniya

2. Mai Fushi,dacin Rai da mummunan tunani

Mutane masu matukar fushi suna damatsala ga rayuwar kowa harma tasu kuwa, domin yawan fushi yana jawo mutum yayi rashin abin daya kamata ya samu,kaga kenan idan kaima kana tare dashi tare zakuyi rashin. Dacin rai kuwa yana jawo yawan fada gamai shi don haka idan abokinka haka yake kayi rashin sa'a Babba domin kullum sai kunyi fada ko kuma saika raba fada Wanda hakanma zubewar daraja ce ko kuma kaima wata rana ka koma kare kamarsa, dadi da kari mai dacin rai bai fiya gaskiya ba. A bangaren mummunan tunani kuwa kullum sai ya jawo magana da cece kuce.wadannan dabi'oi Rabin hankali ne.

3. Mutane masu gadara ko iko

Mutane masu gadara basu da Dadin zama ko kadan domin kowane lokaci zasu rika nuna maka iko da dabi'arsu ta gadara suna ganin kai ba kowa bane duk abin da zaka fada basa ganinsa a matsayin daidai saidai idan su suka fada, su rika son juyaka akan komai. Idan abokin ka ko Wanda kake tare dashi haka yake to daga yau ka kaurace masa domin samun yanci.

4. Masu son abasu (su kuma basa son bayarwa)

Mutane masu son banza kowane lokaci su saidai ka basu su kuma bazasu bayar ba to basu da amfani kona anini,kuma inason mai karatu ya sami irin wadannan mutane rusa mutum suke domin ko durkushewa kayi bazasu tallafeshi ba gudu zasuyi tunda sunsan bazasu sami komai ba. Idan San samu ne Dan uwa ka guji mai irin wannan hali.

5. Mutum marar fata

Mutane marasa fata ko burin wani abu a rayuwarsu rabi suke domin basu da burin zama,mallaka ko samun wani abu a rayuwarsu, domin zaka iya cewa inason zama malami,mai kudi,mai ilimi amma su basu da wannan don haka zama dasu bashi da amfani saboda basu da wani abu da mutum zai karu dasu a tare dasu.


Comments