Min menu

Pages

Kasa mafi kankanta a Duniya

A duk lokacin da aka ambaci sunan kasa mutum zai iya tunanin kamar Nijeriya,America,india,china,Rasha dadai sauran kasashe masu tsarin yanki-yanki ko jaha-jaha ko nau'in yarurruka dabam-dabam.

 Anan abin ba haka yake ba ta fuskar fahimtar menene yake sanya waje a kirashi kasa, ba'asan a Inda aka kwana ba wajen fitar da kasa ta fuskar fadin kasa ko yawan mutane ko ma'adanan kasa da tattalin arziki, a yayin da wasu kasashe suke da girma gaske kamar an wuce gona da iri wajen fitar da fadin da suke dashi kamar kasar America,India,Rasha dadai sauransu.

A duniya akwai wata kasa mai matukar kankanta sama da kowacce kasa Wanda da za'a kwatanta girmanta da babban birnin America (Washington) to baza'a kirata kasa ba saidai kauye, wannan kasa ba wata boyayyar kasa bace face birnin vatikan (Vatican city), Kasar Vatican tana da girman daya kai  murabba'in mile dubu daya (1sqm)wanda a kalla yakai safiya arba'in tara (49ha) a fadin kasa. 



Birnin Vatican kamar yadda sunansa ya nuna ba iya girman kasar ne ba kawai kadan, yawan mutanen ciki ma  bashi da yawa domin idan akayi la'akari dududu da girman kasar yawan mutanen cikinta ma a shekara ta 2020 an kiyasta shi da mutum dubu daya, a shekarar dubu biyu da sha daya (2011) kuma yawan mutane a Vatican gaba daya 793, inda maza suke da yawan mutum 645, mata kuma 148, a shekara ta 2019 kuma yawan mutanen kasar ya karu zuwa 825.

Kasar Vatican city ta samu yanci kanta ne a hannun kasar Rum (italy) a shekarar 1929. Tsarin da Vatican city take dashi na zama Dan kasa shine a haifi mutum a kasar ko Dan kasar yaje wata kasa ya haifi da shima Dan kasar ne. A bangaren yare kuma kasar Vatican city basu da wani tsayayyan yare guda daya saidai sunfi yin amfani da yaren Swiss German, French, Romansh. 



Wajen abin daya shafi tsarin mulki kuwa suna sanya shugaban addini a matsayin Wanda yake sama da kowa a kasar Wanda dukkanninsu kiristoci ne.

Domin kallon bidiyon duba nan




Comments