Min menu

Pages

Mune muka tada bama-bamai a Borno inji shekau

 Mune muka tada bama-bamai a Borno inji shekauJagora kuma shugaban yan ta'addan nan na boko haram wato shekau yace sune suka tada duk wasu abubuwan fashewa a jihar Borno.


Yace basu gajiyawa da kiran duk wani daya yarda da  dabi'un yahudawa ba a matsayin kafiri koda suna sallah sannan ya kara da cewa su kuwa baza su gajiya da kashe duk wasu kafirai ba.


Aikin Allah muke dan haka za muci gaba da kashe ku kafiran bayi.


Sannan ya kara da cewa naji anata cewa wai sojoji sun kwace gona ta a sambisa wannan karya ne basu isa kwace gona ta ba.


Kafirai baza su taba samun nasara akaina ba inji shugaban kungiyar boko haram din.


A kwanan nan anyi ta samun tashin bama-bamai da kuma yawan harbe harben bindinga a wasu garuruwa na jihar Borno wanda har aka raunata mutane da dama.


Sannan yan boko haram din sun samu nasarar kwace garin marte na jihar Bornon kafin sojoji su kwato garin.


Comments