Min menu

Pages

Yanzu yanzu An sace dalibai mata sama da dari uku a jihar Zamfara

 An sace dalibai mata sama da dari uku a jihar ZamfaraMajiya mai karfi ta tabbatar da dauke dalibai mata yan makaranta har guda dari uku.


Daliban wata makarantar sakandire ne ta jengebe ta garin talata karamar hukumar marafa dake jihar Zamfara


Wannan al'amarin ya faru ne dazu dazu da safiyar yau juma'a.


Wani mutumin kauyen kawaye ya shaida cewar yayansa mansura da kuma sakina suna daga cikin yaran da aka sace.


Ina kan hanyata ta zuwa jengebe yanzu domin na gane abinda ya faru da kaina domin an cemin har misalin karfe daya na dare suna bayan makarantar basu yi nisa dasu ba a cewar mutumin.


Lokacin da aka nemi jin ta bakin shugaban yan sandar na yankin SP muhd shehu, to amma dai baice komai ba.


Yace adan bashi lokaci zaiyi magana a cewarsa.


Wannan shine na hudu a garkuwa da mutane da akai mafi girma ga daliban makarantar tun daga na kan daliban makarantar kankara.


Yan bindingar sun shiga makarantar tare da yin gaba da dalibai matan.

Majiya tace kafin yan bindingar sukai da yin awun gaba da daliban saida suka yi musayar wuta da yan bangar garin.

Comments